ALLAH ya yi wa mahaifiyar Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, a yau da yamma.
El-Mustapha da kan shi ne ya ba da sanarwar rasuwar a Facebook, inda ya ce, “Na rasa mahaifiya ta kuma duniya ta, (Gwaggo).”
Ya kuma ce, “Ya Allah ka jiƙan ta, ka gafarta mata kurakuran ta, ka sa aljanna ce makomar ta.
“I will mourn you till my last breath Gwaggo .”
Sai dai bai sanar da lokacin da za a yi jana’iza ba.

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ruwaito yadda Hajiya A’isha ta sa wa ɗan nata albarka a lokacin da aka naɗa shi shugaban Hukumar Tace Finafinai, har aka nuno hotuna inda ta dafa kan sa.
Hoton ne ma El-Mustapha ya yi amfani da shi a soshiyal midiya wajen ba da sanarwar rasuwar ta.

Haka kuma a ranar 27 ga Yuli, 2023 Hajiya da wasu ‘yan’uwan sa tare da iyalin sa sun kai masa ziyarar taya shi murna hade da fatan alheri a ofis ɗin sa.
Allah ya jiƙan ta da rahama, amin.