JARUMAN Kannywood mata sun ƙara wa bikin abokiyar aikin su, Halima Yusuf Atete, armashi a jiya Alhamis.
Ɗimbin ‘yan fim mata sun niƙi gari daga Kano da sauran garuruwa dira a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, inda su ke taka muhimmiyar rawa a bikin shahararriyar jarumar.
Fitattu daga cikin su sun haɗa da Samira Ahmad, Hadiza Gabon, Hauwa Waraka, Fati Baffa Fagge, Fati Yola, Hadiza Kabara, Sadiya Mohammed ‘Gyale’, Maryam Yahaya, Momee Gombe, da Jamila Gamdare.

Zuwan nasu ya ƙara wa bikin armashi matuƙa, musamman shigar da su ka yi jiya ta ‘yan ƙabilar Margi, wato yaren su amarya Halima Atete.
Kamar yadda mujallar Fim ta ba da labari, za a ɗaura auren Halima da sahibin ta Mohammed Mohammed Kala ne a safiyar gobe Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 a masallacin Juma’a na Abuja Sheraton Bus Stop a Maiduguri.

A tsarin bikin, an buga gasar ƙwallon ƙafa a ranar Laraba; jiya aka yi Ranar Margi (Margi Day); sai Daren Larabawa (Arabian Night) da za a yi a daren yau Juma’a, gobe kuma za a ɗaura aure, a yi dina da dare, sa’annan a kai amarya ɗakin ta.
A nan, za a iya ganin hotunan da mujallar Fim ta samu na bikin Ranar Margi da aka yi jiya.








