FITACCIYAR mujallar nan mai suna Tozali, wadda ke ba da labaran bukukuwa da shawarwari kan zamantakewa, za ta karrama fitattun ‘yan Kannywood guda huɗu a bikin karramawar da ta kan shirya a duk shekara mai suna ‘Henna Ball and Awards’.
‘Yan Kannywood ɗin su ne jaruma Rahama Sadau, mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef, mawaƙiya Khairat Abdullahi da jaruma kuma gwanar shirya magana, Maryam Bukar Hassan wadda aka fi sani da Alhanislam kuma babbar ‘yar fitacciyar jarumar nan, marigayiya Hauwa Maina.
Za a karrama Rahama be da kyautar ‘Versatile Actress of the Year’ – Jaruma mafi ƙwarewa a fannoni da dama, yayin da za a karrama Umar da kyautar ‘Music Artist of the Year’ – Gwarzon Mawaƙi na Shekara.
Za a karrama Maryam da kyautar ‘Best Creative Artist’ – Mafi Basira, yayin da aka zaɓi Khairat a matsayin ‘Female Music Artist of the Year’ – Gwarzuwar Mawaƙiya ta Shekara.
Za a yi gagarumin taron karramawar ne a ranar wannan Asabar ɗin, 26 ga Nuwamba, 2023 a katafaren zauren Cibiyar Tarurruka ta Duniya da ke Abuja. Za a fara taron da karfe 6 na yamma.
Shi dai wannan biki, da ma ana shirya shi shekara-shekara, kuma wannan ne karo na 7 da za a yi.
Bugu da ƙari, a kan karrama ‘yan Kannywood a bikin saboda gudunmawar da su ka bayar ga cigaban ƙasa ta hanyar sana’ar su. A baya an taɓa karrama Adam A. Zango, Zaharaddeen Sani, Jamila Nagudu da sauran su.
A bikin na bana, ban da karrama ɗimbin ‘yan Nijeriya da za a yi, za kuma a ƙaddamar da nasarar samun hawa kan satalayit ɗin DSTV da gidan talbijin na Tozali TV ya yi kwanan baya.
A cikin sanarwar da ta ba manema labarai, Manajar Darakta kuma Babbar Shugabar kamfanin mujallar da gidan talbijin ɗin, Barista Maimuna Yaya Abubakar, ta yi bayanin cewa taron karramawar na ‘Henna Ball Awards’ da su ke shiryawa wani sauke nauyi ne ga al’umma wanda mujallar ta fito da shi domin ta taimaka wajen haɓaka al’adun nahiyar Afrika a ɓangarorin yauƙaƙa rayuwar yau da kullum, kwalliya, nishaɗi, shaƙatawa da kuma fasaha.
Hajiya Maimuna ta ce burin taron shi ne ya ba da damar da za a zaƙulo ‘yan Nijeriya masu basira a tallafa masu wajen baje kolin bajintar su a fagen nan mai ban-sha’awa na basirori na Nijeriya.
Ta bayyana cewa taken taron na bana shi ne, “Muhimmancin Zaman Lafiya a Cigaban Ƙasa”, wanda aka zaɓa domin a samo nagartattun hanyoyin magance matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta ta ɓangarori daban-daban.

Ta ce: “Kuma za a yi jan hankali kan matsalar da ‘yan gudun hijira ke ciki, tare da duƙufa kan yin amfani da kuɗin da za a samu daga masu ɗaukar nauyin wasu sassa na wannan taron a tunkari tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ake da su a faɗin ƙasar nan.”
A cewar ta, Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya, shi ne shugaban taron, yayin da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Mista Yakubu Dogara, shi ne zai zama babban baƙo mai jawabi, kuma zai yi magana ne a kan yadda matsalar ‘yan gudun hijira ta zama abin kunya ga Arewa.
A sanarwar, wadda mujallar Fim ta samu, an bayyana cewa za a ƙaddamar da shigar gidan talbijin na Tozali TV cikin tarin gidajen talbijin da ke kan satalayit na DStv.
Tozali TV dai tasha ce mai ɗauke da ababen kallo na nishaɗi da kyautata rayuwa.
Ana kama ta a satalayit ɗin Startimes, Channel na 183, da Canal+ a ƙasar Nijar a kan Channel na 288, yanzu kuma ga ta a kan DStv wanda Hajiya Maimuna ta ce hakan zai taimaka wajen yaɗa al’amuran rayuwar mutanen arewacin Nijeriya da duk inda ake jin harshen Hausa a sassan duniya.
Shugabar ta ce ɗora Tozali TV a kan DStv a Channel na 393 “wani babban zango ne da aka cimmawa, sama da shekara 16 bayan an fara buga mujallar Tozali wadda ta na cikin manyan mujallun Nijeriya masu ba da labaran bukukuwa da tarurruka da zamantakewa.”