• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Marubuciyar farko a Arewa, Hajiya Hafsatu Abdulwaheed, ita ce baƙuwar marubuciyar ƙungiyar ANA Abuja ta watan Nuwamba

by DAGA IRO MAMMAN
November 9, 2023
in Marubuta
0
Fostar gayyata zuwa taron tattaunawa da Hajiya Hafsatu Abdulwaheed da ANA Abuja ta shirya

Fostar gayyata zuwa taron tattaunawa da Hajiya Hafsatu Abdulwaheed da ANA Abuja ta shirya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Abuja, ta bayyana marubuciya ta farko da aka buga littafin ta a Arewa, Hajiya Hafsatu Abdulwaheed, a matsayin baƙuwar marubuciya ta musamman da za a gabatar a taron ta na wata-wata na Nuwamban nan da ake ciki.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta saki a jiya, inda ta ce: “Mu na farin cikin bayyana Hajiya Hafsat Abdulwaheed a matsayin babbar baƙuwar marubuciyar mu ta watan Nuwamba.

“Hajiya Hafsat Abdulwaheed marubuciya ‘yar Nijeriya ce ta musamman, kuma mai rubuta waƙoƙi, ‘yar gwagwarmayar ‘yancin mata, wadda ta bada gagarumar gudunmawa ga harkar adabi da kawo sauyi ga al’umma a rayuwar ta.

“Hajiya Hafsat ta na kan matsayi na musamman a duniyar rubutu a matsayin ta na marubuciya mace ta farko daga Arewacin Nijeriya da aka buga littafin ta na hikaya.

“Ta hanyar rubutun ta, ta bada dama ga mata Hausawa waɗanda ba su da cikakken wakilci a ji muryar su kan abin da su ke buƙata, kuma ta ƙara haskaka al’adu da ɗabi’u daban-daban na Arewacin Nijeriya.

“Rubuce-rubucen ta sun ja hankalin masu karatu a faɗin ƙasar nan da wajen ta, a yayin da ta ke tsara labarai cikin ƙwarewa masu ɗauke da jigogin da su ka jiɓinci daidaituwar jinsina, al’umma, da ƙarfafawa.

“Ban da nasarorin da ta samu a fagen rubutu, Hajiya Hafsat Abdulwaheed ta kuma shiga cikin fafutikar nema wa mata haƙƙin su.

“Irin hoɓɓasa da kuma shauƙin da ta ke da su, su ne su ka ja ta har ta shiga harkar siyasa, inda ta yi bajintar yin takarar zama gwamna a Jihar Zamfara da ke Arewacin Nijeriya a cikin rukunin shekarun 2000.

“Ta hanyar harkokin siyasa da kuma rubuce-rubucen ta, ta taka muhimmiyar rawa a batun ciyar da neman haƙƙin mata da gyaran zamantakewa gaba.

“Abin sha’awa ne ganin cewa ta rubuta littattafai sama da 30, don haka ayyukan adabi da Hajiya Hafsat Abdulwaheed ta yi sun cancanci a jinjina mata.

“Abin alfahari ne ga Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), Reshen Abuja, za ta karɓi baƙuncin Hajiya Hafsat Abdulwaheed a matsayin babbar baƙuwar marubuciyar mu ta watan Nuwamba.

“Shakka babu, abubuwan da ta sani tare da masaniyar ta za su ƙara ilimi tare da ƙarfafa gwiwa ga membobin mu da marubuta masu tasowa da mutane masu sha’awar rubutu, da ma sauran jama’ar gari.

“Mu na cikin ƙosawar tarbar ta domin ta bayyana wa ƙungiyar mu mai daraja yadda ta ke kallon al’amurra da masaniyar ta kan harkar rubutu.”

Ita dai Hajiya  Hafsatu Abdulwaheed, littafin ta na hikaya mai suna ‘So Aljannar Duniya,’ kamfanin Northern Nigerian Publishing Company, Zariya, shi ne ya wallafa shi a cikin 1980.

A taron wata-wata na ƙungiyar ANA ta Abuja, a kan gabatar da marubuci a gaban jama’a don tattaunawa kan ayyukan sa na adabi. Shi wannan da za a yi tare da Hajiya Hafsatu, zai gudana ne a ranar Asabar, 18 ga Nuwamba, 2023, a sakatariyar ANA ta ƙasa da ke cikin Cibiyar Marubuta ta Mamman Vatsa da ke unguwar Mpape a Abuja.

Loading

Previous Post

Babbar furodusa, Fatima Lamaj za ta aurar da ‘yar ta Fa’iza

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da zargin da Peter Obi ya yi mata kan ɗorin kasafin kuɗi

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da zargin da Peter Obi ya yi mata kan ɗorin kasafin kuɗi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!