CIGABAN zamani da kuma sauyawar harkokin yau da kullum a yanzu sun sauya akalar kasuwanci da sana’o’i da al’amuran yau da kullum a kowane ɓangare na rayuwar al’umma. Kamar yadda mu ka gani a kowane lamari na rayuwa, to haka harkar rubutun littattafan Hausa ta samu kan ta a ciki, wanda har ya kai ga harkar ta na neman zama tarihi.
Ganin irin tafiyar ruwa da cigaban zamani ya ke neman yi wa harkar rubutu ne ya sa wasu masu kishi daga cikin tsofaffin marubutan Hausa da kuma masu tasowa su ka yi wani yunƙuri na shirya taro domin samar da wata hanya da za ta ceto rubutun da kuma samar da sababbin marubuta da za su ciyar da harkar gaba ta hanyoyin zamani da ake da su a yanzu da aka koma soshiyal midiya.
A ranar Lahadi, 30 ga Afrilu, 2023 aka gudanar da gagarumin taron a wajen shirya taro na Ali Jita Events Centre da ke Titin Lawan Dambazau a cikin garin Kano. Manyan marubuta daga dukkan sassan Arewa sun halarta domin tattaunawa kan lamuran da ke ci wa harkar rubutun tuwo a ƙwarya.
A taron, mai taken “Marubuta da Cigaban Zamani”, an gabatar da jawabai da kuma tambayoyi daga mahalarta domin kawo mafita da fahimtar juna.

A jawabin sa na maraba da baƙi, ɗaya daga cikin jagororin shirya taron, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka), ya bayyana farin cikin sa da zuwan jama’a masu yawa duk da yake an saka ranar taron da kuma gudanar da shi a ƙurarren lokaci, wanda hakan ya nuna mutane su na kishin rubutun, don haka su ka yi ƙoƙarin zuwa, musamman waɗanda su ka taho daga nesa; har ma daga ƙasar Nijar an samu waɗanda su ka zo.
Anka ya ce: “Mu na fatan za a yi taron lafiya a gama lafiya Allah ya ba mu nasara a kan abin da mu ka sa a gaba.”
Shi kuma a nasa jawabin, Nasir Umar Chiromawa, wanda aka fi sani da Nasir Nid, ya yi jawabi ne kan yadda taron ya samo asali, ya ce, “Farkon tunanin shirya taron ya samo asali ne daga wasu matasan marubuta da su ke rubutu a soshiyal midiya su ka nemi a samar da wani tsari na yadda marubuta za su sauya akalar rubutun su na littattafai da wanda su ke yi soshiyal midiya zuwa yadda za su ci gajiyar sa daidai da wannan zamanin kamar yadda masu rubutun labarin fim su ke cin gajiyar rubutun nasu. Don haka mu ka yi ƙoƙarin samar da wani dandamali da za a haɗu da juna tsakanin tsofaffin marubuta da kuma sababbin da masu rubutun labarin fim don a samar da hanya mai ɗorewa.”
Ya ci gaba da cewa, “Mun yi tunanin mu kai taron ya zama wani bikin Sallah a Babbar Sallah mai zuwa, to kuma sai mu ka ga kamar hakan ya yi nisa, don haka sai mu ka ce za mu shirya wani ɗan ƙaramin taron da zai zama sharar fage na taro na gaba, don haka sai mu ka samar da shi wannan ƙaramin taron.
“Sai dai duk da mun shirya za mu yi ƙaramin taro sai ya zama mutanen da su ka yi rajistar shiga taron sun wuce yadda mu ke tunani. Wannan ya sa daga baya ma mu ka sanar da rufe rajista saboda yawan mutane, domin mun shirya cewa mutane 50 zuwa 100, amma sai mu ka samu sama da 300. Wannan ta sa mu ka rufe rajista saboda yanayin wajen da mu ka tsara gudanar da taron da kuma ba ma buƙatar a yi yawa.
“Don haka mu na godiya ga Allah da ya sa a yanzu mun samu halartar mutane daga jihohi daban-daban, har ma da Jamhuriyar Nijar. Wannan kuma wata alama ce ta yin nasarar abin da mu ka saka a gaba. Da fatan Allah ya yi mana jagora.”
Shi kuma a nasa jawabin mai taken “Sauyawar Marubuta A cikin Zamunna”, marubuci Nazir Adam Salih ya ba da tarihin harkar rubutun littattafan Hausa inda ya ce, “An fara ne daga rubutun littafi a kai wajen bugu ta hanyar ɗaukar nauyi ba tare da kamfani ya tallafa ba, duk da yake a can baya an samu kamfanoni da su ka taimaka su ke buga littattafan marubuta a sanadiyyar gasa da ake sanyawa. Sannu a hankali harkar labarai a littattafai ta dusashe, mutane sun daina karatun littafi, kuma da yawa daga cikin mutane sun alaƙanta hakan da shigowar wayar hannu. Ana ganin ta ɗauke hankalin mafi yawan mutane ta yadda sun fi ba da hankalin su a kan waya fiye da littafin.

“A shekarun 1980 har zuwa1990 da farkon ƙarni na 21, mafi yawan samari su kan yi yawo ne da littafin su a hannu a matsayin ado da burgewa. Amma dai yanzu waya ta karɓe wannan. Don haka a yanzu makaranta sun fi bin rubutun waya fiye da littafin, musamman yaran da aka haifa a shekaru kaɗan kafin samuwar wayar hannu da kuma waɗanda aka haifa bayan samuwar ta.”
Nazir ya ci gaba da cewa: “Wasu daga cikin marubutan da su ke ganin kamar an hana su dama ta hanyar karɓar littattafan su a buga, sai su ka samar wa kan su hanya ta wallafa littattafan nasu a kan yanar gizo kai-tsaye ba tare da sun kashe ko kwabo ba, ko sun nemi taimakon wani. Wannan kuma shi ya haifar da samuwar ‘Online Writers’, yanayin da ya haifar da rubutu marar tsafta. Domin a can baya mu na da hanyoyin tace littafi guda biyu, akwai taron mu na ƙungiyar ANA da za ka je ka karanta a yi maka gyara, sai kuma Hukumar Tace Finafinai. Sannan kuma ko don yadda za a buga littattafai ya shiga hannun jama’a mutum zai ji kunyar saka abin da bai dace ba, saɓanin yanzu da marutan onlayin sun fi yin rubutun batsa kuma an fi sayen sa.
“A can baya marubuta sun taimaki junan su, saboda abu ne aka jima ana yi. Kafin mu an yi wasu da dama, don haka idan ka na buƙatar taimako za ka samu wanda ya fi ka gogewa ya taimaka maka, saɓanin ‘online writers’ da yanzu su ka fara tunda abu ne sabo na zamani, don haka sai su ya su, wannan kuma sai ya haifar da wani tunani na ganin cewa marubutan da su ka gabace su ba sa son su taimaka masu kuma ba sa ba su dama.
“To a yanzu dai zamani ya ci rubutun littafi na gargajiya domin da yawa sun koma rubutun labarin fim mai dogon zango. Wasu kuma sun haƙura da rubutun ma, sai dai halartar taron marubuta don sha’awa ba don su na samun abu a rubutun ba. Haka nan a ɓangaren sabbin marubuta, su da man ba su zo lokacin a buga littattafai a kai kasuwa ba, sun zo ne sun samu matasa ‘yan’uwan su sun ƙirƙiri hanyar rubutun onlayin, a rubuta a nan a sayar a nan. Duk da dai an yi ta ƙoƙarin dawo da rubutun littafi amma dai abin ya ci tura, sai haƙura aka yi.
“Don haka ina fatan wannan taron zai ba mu damar ɗorawa daga inda zamani ya kawo mu, domin zamani abokin tafiya ne, tunda ya zo, mu karɓe shi hannu biyu, kama daga kan rubutun labari mai dogon zango zuwa cinikin littafi a yanar gizo.”
Ita kuma marubuciya Fauziyya D. Sulaiman ta gabatar da jawabi ne mai taken “Daga Ba Kowa Ba Zuwa Tauraro”, inda ta kawo labarin irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa a ƙoƙarin ta zama fitacciyar marubuciya. Ta ce: “Daga lokacin da burin zama wani ya shiga cikin zuciyar ka, a lokacin za ka hango waɗanda su ka yi nasara a wannan fannin da ka ke ƙoƙarin shiga har ka fara tunanin zama kamar su ko ma ka fi su. Duk da na rubuta littafin da ba ni da kuɗin bugawa da kai na, amma ban taɓa karaya ba. Domin na karanta labarin wasu marubuta a nan ƙasar da kuma ƙasashen waje da su ka samu tasgaro da fari amma dagewa ta sa su ka yi nasara.
“Don haka ina kira ga masu rubutun onlayin da su fito da sunan su da su ke ɓoyewa, domin fitowar sunan su zai ba su damar da tunanin su bai taɓa ba su ba.”
Ita kuma marubuciya Maimuna Idris Beli ta yi jawabin ta ne a game da yadda ake cin gasa, inda ta kawo hanyoyin da su ka haɗa da dagewa da saka tunanin yin nasarar da kuma yin rubutu
mai ma’ana da zai zama karɓaɓɓe a wajen jama’a.

Su ma marubutan onlayin irin su Hassana Labaran Ɗanlarabawa da Na’ima Sulaiman Sarauta an ba su ɗan lokaci su ka yi bayani a game da harkar rubutun onlayin da kuma kasuwancin sa.
Daga ƙarshe an yi tambayoyi da kuma sanya albarka daga bakin manyan baƙin da su ka halarta.
Taron ya gudana cikin tsari da kuma kwanciyar hankali, kuma mahalarta sun gamsu da abubuwan da aka tattauna tare da fatan Allah ya kai mu haɗuwa ta gaba.




