A ranar Lahadi, 8 ga Oktoba, 2023 membobin wata ƙungiya mai suna Gamayyar Marubutan Jihar Kano (GAMJIK) su ka kai wa uban ƙungiyar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ziyara domin yi masa ta’aziyyar rasuwar mariƙin sa.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba da labarin rasuwar Alhaji Yusha’u Mustapha Mai Dabino Sani Mainagge, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 30 ga Satumba, 2023.
Tawagar marubutan, a ƙarƙashin jagorancin Mukhtar Musa Ƙarami, sun yi addu’a ga mamacin da sauran dukkan Musulmi da su ka riga mu gidan gaskiya, tare da yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya game da halin da mu ka samu kan mu a ciki.
Bayan ta’aziyyar, sun kuma tattauna kan abin da ya shafi cigaban ƙungiyar da wasu batutuwa na adabi.
Uban ƙungiyar ya raba wa dukkan waɗanda su ka samu zuwa wannan taro littafin sa mai suna ‘Malam Zalimu’.