ALLAH ya azurta furodusa kuma jarumi a Kannywood, Sabi’u Muhammad Gidaje, da samun ɗa namiji.
Wani abin ban-al’ajabi shi ne an haifi jaririn da sunan Allah a kunnen sa.
Maiɗakin Sabi’u, Hajiya Bilkisu, ta haifi yaron da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Juma’a, 6 ga Oktoba, 2023 a asibitin gwamnati mai suna Yusuf Ɗantsoho, wanda aka fi sani da Asibitin Dutse, da ke Tudun Wada, Kaduna.
Sabi’u ya raɗa wa jaririn suna Muhammad, wanda sunan mahaifin sa marigayi Alhaji Muhammad Gidaje ne.

Sai dai kuma jarumin ya shaida wa mujallar Fim cewa ba za a yi taron suna ba sai ƙarshen wannan wata, sakamakon aiki da aka yi wa maiɗakin tasa.
A yanzu ‘ya’yan jarumin biyu, wato Islam da Muhammad.
Allah ya raya su baki ɗaya, ya albarkaci rayuwar su, amin.