ALLAH ya azurta mawaƙin Kannywood, Zayyanu Abubakar Extra, da maiɗakin sa, Nana Firdausi, da samun ɗa namiji.
Nana Firdausi ta haihu ne a ranar Lahadi, 18 ga Yuni, 2023 a wani asibitin kuɗi mai suna ‘Maryam Murtala Hospital’ da ke Amingo by Express, Sabon Garin Tudun Wada, Kaduna, bayan ta sha fama da naƙuda har kwana biyu da wuni ɗaya a asibitin Barau Dikko Teaching Hospital da ke Titin Yakubu Gowon, Kaduna.
Extra ya shaida wa mujallar cewa, “Ganin ta ɗauki kwana biyu da wuni ɗaya ba ta haihu a asibitin ba ne, kuma su na ta yi mana wasa da hankali, ya sa ɗauke ta mu ka mai da ta na kuɗi, inda a cikin minti 30 aka yi mata aiki (CS) aka ciro yaron.”
An dai raɗa wa jaririn suna Muhammad Nasir, amma ana kiran sa da Munif.

Sai dai kuma Extra ya ce ba a ranar Lahadi mai zuwa za a yi taron suna ba, sai maijego ta warware, bayan Sallah in Allah ya kai mu.
Angon ƙarnin ya yi wa Allah godiya da ya azurta shi da ɗa. Ya ce, “Wallahi sai yanzu na ji abin da iyayen mu su ke ji kan mu. Haka na ke zama in riƙa kallon hoton sa har sai waya ta ta ɗauke. Lokacin da aka haife shi, aka ce in zo an haihu, da ana miƙo min yaron yi na ke ina cogewa; mamaki kawai na ke yi wai ɗan wani aka ba ni in riƙe ko nawa ne?”
Allah ya raya Muhammad Nasir, amin.