A WANNAN zamanin akwai haziƙan mawaƙa da ake yayi, waɗanda su ke jan zaren su a harkar waƙoƙin finafinan Hausa. Hussaini Danko ya na ɗaya daga cikin su. A yanzu ana iya saka shi a sahun farko na mawaƙan da ke haskawa. Hussaini ya yi waƙoƙi fitattu da dama, musamman a kamfanin Adam A. Zango.
Mujallar Fim ta tattauna da shi game da yadda aka yi ya fara waƙa, tarihin sa da sauran su.
FIM: Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunan ka da tarihin rayuwar ka a taƙaice.
HUSSAINI DANKO: Assamu alaikum. Suna na Hussaini Abubakar Hussaini, wanda aka fi sani da Hussaini Danko.
Asali na ni mutumin Jos ne. An haife ni a garin Jos, na yi makarantar firamare da sakandire duk a garin Jos.
FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka cikin wannan sana’a ta waƙa?
HUSSAINI DANKO: Idan na ce maka ga yadda aka yi na tsinci kai na a harkar waƙa, to na yi ƙarya. Kawai ni dai na gan ni tsamo-tsamo a cikin ta.
FIM: Ko za ka iya tuna waƙar da ka fara yi?
HUSSAINI DANKO: Waƙar farko wadda na fara yi sunan ta “Dawo Dawo”, wadda na ke cewa, “Dawo dawo masoyi na dawo ba za ni dawo ba, laifin da nai ka zamto yafewa wallahi na tuba.” Wannan ita ce waƙar da na fara yi ta farko a duniya.
FIM: Aƙalla yanzu ka yi waƙoƙi kamar guda nawa?
HUSSAINI DANKO: Gaskiya ba zan iya kawo adadin su ba, amma sai dai kawai na ƙiyasta in ce kamar guda ashirin.
FIM: A cikin waƙoƙin da ka yi wacce ce bakandamiyar ka?
HUSSAINI DANKO: Ni har yanzu a cikin waƙoƙi na ban yi wata bankadamiya ba, wadda zan ce na fi son ta. Har yanzu dai ina kalallaɓawa ne; ban yi bakandamiya ba.
FIM: Me ya sa ake kiran ka da “Hussainin Danko”?
HUSSAINI DANKO: To, Ibrahim Danko dai ubangida na ne, ni kuma na zauna a ƙarƙashin sa ne. To a lokacin idan aka yi tambaya aka ce, “Za mu je aiki wajen su Hussaini,” idan aka ce, “Wanne Hussaini?” sai a ce “Hussainin Danko.” To daga nan dai sunan ya samo asali ake kira na Hussainin Danko.
FIM: Wasu su na ganin kamar ka na ɗaukar irin salon Abubakar Sani ka na waƙa da shi. Shi ma ka na da alaƙa da shi ne?
HUSSAINI DANKO: To maganar wai a ce ina ɗaukar salon Abubakar Sani wannan ba gaskiya ba ne. Salon Abubakar Sani daban, salo na daban, sai dai da ya ke ni mutum ne mai neman shawara don haka idan na yi waƙa ina kai wa Abubakar Sani ya saurara, idan ya ji ta zai iya ce min a gyara kaza da kaza. Sannan akwai alaƙa ta mutuntaka tsakani na da shi.
FIM: Ko akwai wani ƙalubale da ka taɓa fuskanta dangane da sana’ar ka ta waƙa?
HUSSAINI DANKO: Gaskiya ni babu wani ƙalubale da na taɓa fuskanta har yanzu.
FIM: Ta ɓangare nasarori kuma fa?
HUSSAINI DANKO: To, nasarori alhamdu lillahi! Ina da su da dama, don yanzu haka a kan nasarar na ke: na yi aure, na yi gida, na yi mota, kuma na buɗe situdiyo nawa na kai na, kuma ga masoya Allah ya ba ni. Duk waɗannan nasarori ne waɗanda na ke alfahari da su.
FIM: Kamar waɗanda su ke jin waƙoƙin ka ba su san ka a fuska ba, ta yaya za a yi su gane ka?
HUSSAINI DANKO: To in-sha Allahu ni ma ina nan ina da niyyar fito da album na bidiyo mai suna ‘Hali Da Kama’. Idan na kammala ya fita kasuwa duk wanda ya kalla zai ga ko wanene Hussaini Danko.
FIM: To, me ya sa ka fi ba ɓangaren waƙa ƙarfi?
HUSSAINI DANKO: To abin da ya sa na fi ba waƙa ƙarfi da kuma muhimmanci, na ɗauke ta ita ce sana’a ta, wadda na ke cin abinci da ita.
FIM: Wane kira ka ke da shi ga ’yan’uwan ka mawaƙa?
HUSSAINI DANKO: To kiran da na ke da shi ga ’yan’uwa na mawaƙa shi ne mu ƙara haɗa kai kuma mu zage damtse, sannan mu san wannan abin da mu ke yi mu na yi ne don al’umma, ba wai don kan mu ba.
Sannan mu riƙa gyara kalaman mu domin ita waƙa kalma ce; akwai kalmar da idan ka fidda ta ba za ka gane abin da ke cikin ta ba sai nan gaba. Idan mutum ya na abu ya dinga hangen nan gaba, saboda ba ka san yadda rayuwa za ta zamo maka ba; akwai hawa kuma akwai sauka. Ita rayuwa ka riƙa hangawa; don na zama wane bai kamata na wulaƙanta wane ba, in riƙa ɗaukar kai na ni wani ne.
Ba ina magana kan kai na ba ne, a’a, ina magana ne kan mu mawaƙa. Akwai waɗanda su ke da wannan wulaƙancin, don mutum ya samu dama shi kenan ya samu damar taka mutane da wulaƙanta su. Duk wannan ba na mawaƙi ba ne, mawaƙi na kowa ne ba wai ka ware ka ce sai wanda ka sani za ka yi mu’amala da shi ba. Rayuwar mawaƙa da rayuwar ‘yan fim ba haka take ba, ina kira ga dukkan mu mu gyara.
FIM: Wane saƙo ka ke da shi ga masoyan ka?
HUSSAINI DANKO: To saƙon da na ke da shi shi ne su ci gaba da yi mana addu’a. Sannan kuma su zage damtse su tsaya yadda su ke; ina yi masu fatan alheri, Allah Ya bar mu tare.