INNA lillahi wa inna ilahi raji’un! Allah ya yi wa mawaƙi a Kannywood, Mu’azu Muhammad Birniwa, wanda aka fi sani da El-Mu’az, rasuwa a daren yau Laraba.
Wata majiya ta shaida wa wakilin mujallar Fim cewa Elm-Mu’az ya halarci wurin wasan ƙwallon ƙafa na bikin mawaƙi Auta Waziri, wanda aka yi a Hamada Pitch da ke otal ɗin Hamdala a Titin Muhammadu Buhari (Waff Road), sai a nan ya yanke jiki ya faɗi, daga nan aka ɗauke shi zuwa wani asibiti mai suna Dialogue, inda aka tabbatar da rasuwar sa.
Marigayin yana ɗaya daga cikin waɗanda suka buga ƙwallo a filin kafin rasuwar sa.

El-Mu’az sanannen mawaƙi ne, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Birniwa, Jihar Jigawa, amma haifaffen Kaduna, inda a nan ya yi dukkan rayuwar sa.
Allah ya jiƙan sa, amin.