FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Abdussamad Adam, wanda aka fi sani da suna Abdul Respect, shi ma ba a bar shi a baya ba a auren da ake yi na ƙarshen shekara.
A ranar Lahadi, 15 ga Disamba aka ɗaura auren sa da amaryar sa, Hassana Abubakar Bulama, a Hotoro Tsamiyar Boka Layin Maƙabarta, da misalin 11 na rana.
Jama’a da dama sun halarta.
Tun kafin ranar, angon ya shirya taron biki a ranar Asabar a Tauraruwa Events Centre da ke Farm Centre a cikin garin Kano, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarta domin taya shi murna.
Jaruman da suka halarta sun haɗa da Ali Nuhu, da Momee Gombe, da kuma mawaƙa.



Da fatan Allah ya sanya albarka.