• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Idris na so ‘yan sanda su rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa

by WAKILIN MU
November 19, 2024
in Nijeriya
0
Minista ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al’umma

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya (NPF) da ta rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa.

Ya bayyana cewa rungumar ƙa’idojin Yarjejeniyar zai inganta kallo da fahimtar da jama’a suke yi wa rundunar.

Sanarwar da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar ta nuna cewa ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron ƙara wa juna sani na jami’an hulɗa da jama’a na ‘yan sanda wanda aka yi a Asaba, Jihar Delta.

Idris, wanda ya samu wakilcin Darakta-Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba-Ndace, ya ce: “An ƙirƙiri Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa a matsayin tsarin ayyana mu a matsayin ’yan Nijeriya da kuma tabbatar da manufofin mu na gaskiya a cikin muradin mu.

“Tana cike giɓin da aka samu wajen neman haɗin kan ƙasa, cigaban al’umma, da kishin ƙasa mai ɗorewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

“Don haka ina amfani da wannan dama don yin kira ga Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da ta rungumi yarjejeniyar ɗa’ar da zuciya ɗaya, tare da yin amfani da ita don ƙirƙirar sabon labari na Nijeriya.

“Dole ne dukkan mu mu gane cewa ‘Yan Sandan Nijeriya na kan gaba wajen yadda ake kallon ƙasar mu a cikin ƙasa da kuma duniya.”

Ministan ya bayyana irin rawar da ‘yan sanda ke takawa a matsayin hukumar tsaro ta farko da ke mu’amala da al’ummar Nijeriya.

Ya yi nuni da cewa aikin rundunar ya wuce tabbatar da bin doka da oda, ya kai ga kare rayuka, mutunci, ‘yanci, da dukiyoyin ‘yan ƙasa, inda ya jaddada muhimmancin yin aiki da kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zamantakewa da ‘yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa aikin ‘yan sanda mai inganci ya dogara ne da fahimtar juna da kuma wani nauyi da ya rataya a wuyan ‘yan sanda, gwamnati, da jama’a, yana mai cewa amanar jama’a ita ce ƙalubale mafi girma da rundunar take fuskanta a yau.

Ya ce: “A cigaban da muke samu a matsayin mu na ƙasa da kuma cigaban mutuncin mu, ‘yan sanda sun yi fafutuika wajen mu’amala da jama’a, musamman saboda saɓani na kare haƙƙin jama’a da tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

“Wannan gwagwarmaya ta ƙara zama ƙalubale saboda akwai wasu abubuwan cikin gida masu hani da ke dagula tasirin ƙwararrun ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukan su.”

Ministan ya yaba wa shugabannin NPF da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, bisa shirya taron.

Ya kuma amince da daidaita ayyukan rundunar tare da manufar Shugaba Bola Tinubu ta samun ingantaccen aiki.

Loading

Tags: 'yan sandaJibrin Baba NdaceMohammed Idrisyarjejeniyar ɗa'a
Previous Post

KILAF Award 2024: Mun shirya tsaf, lokaci muke jira, inji Galadima Muhammad

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi jimamin rasuwar Babban Limamin Minna

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya yi jimamin rasuwar Babban Limamin Minna

Ministan Yaɗa Labarai ya yi jimamin rasuwar Babban Limamin Minna

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!