• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

KILAF Award 2024: Mun shirya tsaf, lokaci muke jira, inji Galadima Muhammad

by MUKHTAR YAKUBU
November 18, 2024
in Labarai
0
KILAF Award 2024: Mun shirya tsaf, lokaci muke jira, inji Galadima Muhammad

Galadima Muhammad, Daraktan shirya taron KILAF Award 2024

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A yayin da ya rage ƙasa da mako guda a shiga gagarumin Bikin Baje-kolin Finafinai na Harsunan Afrika na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ na wannan shekarar, tuni duk abubuwa sun fara kammala, domin za a gudanar da taron bikin daga ranar 25 zuwa 30 ga Nuwamba nan da muke ciki.

A wata tattaunawa da mujallar Fim ta yi da daraktan shirya taron bikin, Galadima Muhammad, ya bayyana mana cewa: “A yanzu shirye-shirye ya yi nisa, mu yanzu kwamitin taron muna ta shirye-shirye don ganin abubuwan sun tafi kamar yadda muka tsara. Kamar ka ga a cikin abubuwan da za a gabatar a taron akwai horaswa da za a yi a kan harkar fim na babban aji wato ‘Master Class’ na tsawon kwana uku wanda za a gudanar a Dangote Business School.

“Sannan muna da wani taro na ‘Woman in Media Business Summit’ da wasu NGO suka shigo ciki za mu yi haɗaka da su tare da haɗin gwiwa da wata ƙungiya a Uganda.

“To bayan wannan kuma muna da wani ɓangare na horaswa duk a cikin taron da za a gudanar tun daga ranar 25 zuwa 30, wanda muke buƙatar duk ‘yan kasuwa za su zo su yi rajista don su zo su yi bajekolin kayansu, don masu sha’awa su zo su saya saboda kasuwa ce.

“Sannan mun tsara finafinai da za a kalla, wanda za a kalli fim ɗin Kabiru Musa Jammaje ‘Princess Of Galma’ sai kuma wani fim daga Uganda shi ma za a kalla. Haka nan akwai wasu finafinai guda biyu daga Maroco ɗaya kuma daga Ruwanda, kuma shi na Ruwanda ma furodusan fim ɗin ma zai zo, saboda yana so idan an kalla a yi masa tambayoyi ya bayar da amsa.

“Haka nan kamfanin Movie Image sun shirya wani fim Tarnaki, shi ma za a kalla tare da buɗe ƙofar tambayoyi, sannan akwai taro a gidan Gwamnatin Jihar Kano, don wannan karon taron bayar da Award za a yi shi ne a babban ɗakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kano, muna sa ran mu karɓi baƙuncin Ministar Al’adu, Hannatu Musawa, a wajen rufewar.

“Hakan a wajen buɗewa tun da farko muna sa ran Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris, su kasance manya a wajen buɗewar.

“Sannan muna sa ran akwai Royal Dinner wadda Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll zai halarta. Kuma muna da zagayen buɗe Ido a garin Kano da baƙi za su zagaya su ga irin al’adun mu da kuma kayayyakin mu na tarihi.

“Kuma Alhamdulillah, mun samu mutane da dama da za su shigo Kano don halartar taron. Kamar daga Jihar Zamfara kaɗai akwai mutane 40 da suka yi rajista za su zo da sauran jihohi da dama, banda ma waɗanda za su zo daga ƙasashe daban-daban na duniya.

“Haka nan a ɓangaren ku na ‘yan jarida akwai ‘yan rediyo da talbijin da kuma kafafen yaɗa labarai na soshiyal midiya duk mun zauna da su. Haka nan akwai National Art Gallery wanda su ma suna daga cikin waɗanda muka yi haɗin gwiwa da su. Da kuma Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano su ne duk za su ɗauki ɗawainiyar yawo da mutane, don haka duk wani shirin ma a yanzu ya yi nisa duk wani masaukin baƙi da za mu yi amfani da shi mun riga mun tanade shi, da wajen da za a ci abinci duk an samar da su, duka dai a yanzu, lokaci kawai muke jira.

“Don haka a yanzu muna kira ga mutane kada baƙi su zo garin mu su fi mu rawa. Don mun gani a gasar finafinai da aka shigar ina ganin fim ɗin Hausa ba su fi guda biyu ba a cikin finafinai guda 511 da suka shiga gasar a wannan shekarar.

“Fim ɗin ‘KAKA’ na Aboki shi kaɗai ne a gasar, kuma bai kamata a ce wannan damar ta zo amma Kannywood da ya kamata a ce sun shigo, sai ya zama ba su shigar da finafinan su ba. To ya kamata a ce wajen taron su zo, saboda dama ce ta samu da baƙi za su zo wadda za ta taimakawa wasu daga cikin mu, su samu dama da za a yi haɗin gwiwa da su a shirya fim.

“Don muna sa ran mutane daga Kwatano, Benin, Ruwanda, Uganda, Afirika ta Kudu, da sauran manyan ƙasashe na duniya, don haka bai kamata mu bar wannan dama ta suɓuce mana ba.”

Loading

Tags: KILAFKILAF 2024
Previous Post

Jaruma Sapna Aliyu Maru ta kammala karatun ta na digiri

Next Post

Minista Idris na so ‘yan sanda su rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Minista ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al’umma

Minista Idris na so 'yan sanda su rungumi Yarjejeniyar Ɗa'a ta Ƙasa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!