• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista na so masu zanen gine-gine su riƙa bayyana kyakkyawan tarihin mu

by WAKILIN MU
February 2, 2024
in Nijeriya
0
Minista na so masu zanen gine-gine su riƙa bayyana kyakkyawan tarihin mu

Minista Idris tare da

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Minista Idris tare da Madam Mobolaji Adeniyi

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga Hukumar Masu Zanen Gine-gine ta Ƙasa (National Institute of Architects) da su shiga sahun gaba wajen yin azamar farfaɗo da kyawawan fasalin gine-ginen da ke ƙara haskaka tarihin Nijeriya.

Idris ya ce irin waɗannan gine-gine masu fasalin daɗaɗɗen tarihi su ne ke nuna irin ƙasaitar kowace ƙasa.

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Suleiman Haruna, ya faɗa a cikin wata sanarwa da sa wa hannu, cewa ministan ya bayyana hakan ne a yayin da tawaga daga hukumar ta kai masa ziyara, a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar cibiyar ta himmatu wajen taskace kayayyakin tarihi musamman masu nuna ƙasaitattun gine-gine masu tarihi domin yawancin ‘yan Nijeriya ba su ma san tarihin ƙasaitattun gine-ginen da ke yankunan su ba.

Idris ya ce: “Shin ko kun san cewa ofishin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) a yanzu haka a Abuja, ya taɓa zama ofishin tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Shehu Shagari?

“To hatta ɗakin taro na NOA ɗin ya taɓa zama Zauren Taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, inda ministoci su ka riƙa yin taron su da Shugaban Ƙasa.

“Idan ka ziyarci ofishin NOA a yau ɗin nan, za ka ga ita kan ta kujerar da marigayi Shugaba Shagari ya riƙa zama a kan ta, lokacin ya na shugaban ƙasa.”

Idris yi kira ga hukumar ta ƙwararrun masu zanen gine-ginen da su ci gaba da tuntuɓa da kuma yin aiki tare da ma’aikatar sa wajen ƙoƙarin sake wayar da kan jama’a, domin ɗabbaƙa kyawawan al’adun mu.

Ya kuma yi tsinkayen cewa jama’a su ne mafi tasirin al’adu da kowace ƙasa za ta yi alfahari da su.

Ya ƙara da cewa idan jama’a su ka rasa kyawawan ɗabi’u da ƙarancin wayewar kai a matsayin su na al’umma, to duk wani ƙoƙarin da ake son a cimma, ba zai yi nasara ba.

Ministan ya yi ƙorafi dangane da munanan ɗabi’un wasu marasa kishi, waɗanda ba su darajta gine-ginen tarihin ƙasa da sauran ababen da ke haskaka kyakkyawan tarihin mu a matsayin ƙasa, musamman Tutar Nijeriya, Tambarin Nijeriya, fasfo na shaidar ɗan ƙasa da sauran su.

Minista tare da shugabannin Hukumar Zanen Gine-gine ta Ƙasa

Haka kuma ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ɗau himmar kawo kyakkyawan sauyi a zukatan jama’a, dalili kenan ma ya bayar da fifiko da maida hankali kan Shirin Wayar da Kai a matsayin sabon aiki wurjanjan da ya ɗora wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai.

Ita kuwa Shugabar Hukumar Masu Zanen Gine-gine ta Ƙasa, Mobolaji Adeniyi, ta nuna cewa a shirye hukumar take wajen haɗa kai da haɗa ƙarfi da Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai domin samun nasara wajen wayar da kan jama’a, musamman a ɓangaren kamfen don nuna wa mutane illolin da ke haddasa rugujewar gine-gine, haɗarin da ke tattare da gini maras inganci ko kayan gini marasa nagarta da sauran hanyoyin da za a taskace gine-gine masu tarihi a ƙasar nan, musamman a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Loading

Tags: architectsMobolaji AdeniyiMohammed Idriszanen gine-gine
Previous Post

Mawaƙin hip-hop, DJ AB, ya samu digiri daga Jami’ar Ahmadu Bello

Next Post

Ciyamomin MOPPAN na jihohi sun taya Habibu Barde murnar zama shugaban ƙungiyar

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Next Post
Ciyamomin MOPPAN na jihohi sun taya Habibu Barde murnar zama shugaban ƙungiyar

Ciyamomin MOPPAN na jihohi sun taya Habibu Barde murnar zama shugaban ƙungiyar

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!