• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 3, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya na so a kula da lafiyar gajiyayyu

by DAGA WAKILIN MU
September 30, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Hajiya Sadiya Umar Farouq

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji, da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira da a kare haƙƙoƙin dattawan ƙasar nan.
 
Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ake gudanar da taron Ranar Tsofaffi ta Duniya, wanda aka yi a Abuja a ranar 30 ga Satumba, 2020.
 
A taron, inda Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Alhaji Nura Alkali, ya wakilce ta, ministar ta ce mutane masu yawan shekaru su na taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma a matsayin shugabanni, waɗanda ke kular mana da al’adun mu, kuma abin koyi waɗanda ya kamata a riƙa girmama su tare da yin haƙuri da su da ba su girma.
 
Ta ce, “Ranar Tsofaffi ta Duniya ta bana ta zo a kan kari, ganin cewar ana fama da cutar korona wadda ta shafi mutane masu yawan shekaru ƙwarai da gaske a duk faɗin duniya.
 
“Annoba kan fi shafar mutane masu yawan shekaru tare da saka su cikin babban haɗari domin cuta ta fi kama su, ta jiki da ta tunani tare da ja masu ɓarnar kuɗi wanda ya haɗa da a zambace su tare da mantawa da su. Abin baƙin ciki shi ne da yawan su cuta kan yi saurin kama su, sannan an fi nuna masu bambanci da cutarwa saboda rashin lafiya da sauran lamurran damuwa da kan shafi tsufa.
 
“A wannan rana da aka ware domin tunawa da mutane masu yawan shekaru, tare da kula da gudunmawar su da al’umma, ina kira a gare mu baki ɗaya da mu girmama su, mu darajta su, kuma mu yi haƙuri da su.
 
“Tsufa ba cuta ba ne ko kasawa, amma albarka ne kuma lokaci ne a rayuwa da duk mu ke so mu cimmawa.”
 
Sadiya Umar Farouq ta gode wa mutane masu yawan shekaru saboda gudunmawar su wajen gina ƙasa, kuma ta tabbatar masu da cewa ma’aikatar ta za ta goya masu baya domin su samu sauƙin gudanar da rayuwar su.
 
Haka kuma ta nanata sadaukarwar gwamnati ga kafa tare da fara aiwatar da Cibiyar Tsofaffi ta Ƙasa (National Senior Citizen’s Centre) wadda ake sa ran za ta samar da horo da damarmaki wajen fito da ayyuka da shirye-shirye domin ‘yan ƙasa masu yawan shekaru.”
 
Jigon ranar ta bana shi ne “Annobobi: Su Na Sauya Yadda Mu Ke Kula Da Yawan Shekaru Da Tsufa Kuwa?”

Loading

Previous Post

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

Next Post

Ilimin Aruli a ƙasar Hausa

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Next Post
Ilimin Aruli a ƙasar Hausa

Ilimin Aruli a ƙasar Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!