• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministan Yaɗa Labarai na so masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta su riƙa nuna Nijeriya da kyau

by WAKILIN MU
October 25, 2024
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai na so masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta su riƙa nuna Nijeriya da kyau

Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabin sa a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu ƙirƙira da masu tasiri a shafukan sada zumunta da su rage munanan kalamai kan Nijeriya tare da fifita muradun ƙasar ta hanyar bin ƙa’idojin ɗa’a wajen gudanar da ayyukan su.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin Makon Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai na Duniya na Ƙasa na 2024 mai taken “New Digital Frontiers of Information: Media and Information Literacy for Public Interest Information” wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya, Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya.

A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar, Idris ya jaddada muhimmancin daidaita suka da kishin ƙasa, inda ya buƙaci masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta da su yi la’akari da muradun ƙasa yayin yaɗa bayanai.

Ya bayyana cewa, “Yana da muhimmanci mu riƙa suka da kuma sanya gwamnati da sauran shugabanni su yi bayani domin aikin kafafen yaɗa labarai kenan…Amma kuma yana da matuƙar muhimmanci a wajen bayar da rahoto, mu fifita muradin ƙasa.”

“Ina sake maimaitawa, ba za mu iya tsammanin girma da kuma samun mutane su zo su zuba jari a ƙasarmu ba yayin da duk abin da muke turawa waje a kowane lokaci ba shi da kyau. Akwai labarai masu kyau da yawa da ke fitowa daga Nijeriya kuma ya zama wajibi mu kasance masu kishin ƙasa yayin da muke bayar da rahoto domin Nijeriya ta kai ga inda take so ta kai na wadata da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a kai,” inji shi.

Ministan ya yi Allah-wadai da yaɗuwar labaran ƙarya a shafukan sada zumunta, inda ya yi gargaɗin cewa, idan ba a daƙile ba, hakan na haifar da barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ya bayyana cewa, “Duk wanda ke da kwamfutar tafi-da-gidan-ka ko wayar android zai iya zama mai samar da labarai, wanda zai iya isa ga mutane masu yawa. Sai dai, wannan shimfiɗar wuri na dijital… yana haifar da matsaloli masu muni, musamman tare da yaɗuwar bayanan ƙarya.”

Idris ya yabawa UNESCO bisa ƙoƙarin da take yi na yaƙi da labaran ƙarya a Nijeriya ta hanyar kafa Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya.

Ya ba da sanarwar cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai tare da haɗin gwiwar Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) na ci gaba da mayar da cibiyar ta zama Cibiyar UNESCO ta Rukuni na 2.

A lokacin da ake buga taken Nijeriya

Wakilin UNESCO a Nijeriya, Abdourahamane Diallo, ya kuma jaddada muhimmancin shigar da Ilimin Yaɗa Labarai (MIL) cikin tsarin karatun Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya, Farfesa Olufemi Peters, ya gode wa Ministan bisa goyon bayan da yake bai wa jami’ar wajen ƙarfafa ayyukan Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya da ke cikin jami’ar.

Minista tare da manyan baƙi bayan an gama buɗe taron

Loading

Tags: labaran ƙaryaMohammed IdrisNOUNUNESCOYaɗa Labarai
Previous Post

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Zulai Illah, ta riga mu gidan gaskiya

Next Post

An kammala taron horas da ‘yan Kannywood kan inganta sana’ar su

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
An kammala taron horas da ‘yan Kannywood kan inganta sana’ar su

An kammala taron horas da 'yan Kannywood kan inganta sana'ar su

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!