• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An kammala taron horas da ‘yan Kannywood kan inganta sana’ar su

by MUKHTAR YAKUBU
October 27, 2024
in Labarai
0
An kammala taron horas da ‘yan Kannywood kan inganta sana’ar su

Wasu daga cikin manyan baƙi a wajen taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Taron horas da ‘yan Kannywood na tsawon wuni biyu da aka shirya daga ranar 23 zuwa 24 ga Oktoba ya samu yabo daga mahalarta taron da suka zo daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Kannywood TV dake titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano bisa jagorancin Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa da kuma kamfanin sadarwa na duniya, Google.

A yayin gudanar da taron, manyan masana akan harkokin fim da Kasuwancin sa a duniya sun gabatar da jawabai a kan yadda Kasuwancin fim yake tafiya a yanzu a duniya.

Tun da farko da yake jawabi a kan manufar shirya taron, Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), Dakta Husseini Shu’aibu, ya shawarci jagororin shirya finafinai a Nijeriya da su samar da waɗanda za su riƙa jawo hankalin masu zuba hannun jari don ci gaban masana’antar.

Ya ce, “Duk da cewa masana’antar fim a Nijeriya tana samun ci gaba, amma akwai buƙatar a rinƙa samar da finafinai masu ma’ana da za su taimaka wajen yin nasara a kasuwancin masana’antun finafinai.”

Ya ƙara da cewa, “Ana da buƙatar samun nuna ƙwarewa yayin shirya fim ta yadda hakan zai taimaka wa bunƙasar masana’antar da ma kasuwancinta, domin akwai masu shirya fim da dama da ba sa gabatar da finafinan su ga hukumar don ta yi nazari game da su wanda yin hakan ya saɓa wa doka kuma abu ne da yake haifar da koma baya ga harkar fim a Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa, “Mu na ci gaba da ƙoƙari wajen ganin an tabbatar da masu shirya fim su na samun taimako na kayayyakin aiki da kuma kuɗi don haɓaka harkokinsu. Don haka masu harkar fim abu ne da yake muhimmanci mu samar da hanyar da za ta inganta sana’ar tare da bin doka da oda.”

Shi ma da yake nasa jawabi, jigo a cikin harkar fim ta Nijeriya , Abdulkareem Mohammed, ya bayyana taron a matsayin wani dandamali na kawo sauyi a cikin harkar fim a ƙasar nan, inda ya ja hankalin mahalarta taron da su yi amfani da abubuwan da za a gabatar a wajen domin cin moriyar sana’ar su yadda za su yi daidai da takwarorin su na duniya.

Dakta Ahmad Muhammad Sarari, shi ma ya yi kira ga masu harkar fim da su karɓi ci gaban zamani domin ci gaban masana’antar fim ta Nijeriya.

Bayan kammala jawabi, an shiga horas da mahalarta taron inda aka raba su kaso biyu. An horas da kashi na farko kan yadda tsarin rubutun labarin fim yake da yadda ya kamata masu rubutun za su yi amfani da salo na zamani wajen tsara labarin fim.

Sai kuma kaso na biyu da aka horas a kan tsara fim da ɗaukar hoto da saddabaru da ake yi a cikin fim wanda aka kammala da misalin ƙarfe uku na rana.

Taron ya cigaba a rana ta biyu da misalin ƙarfe 10 na safe. Kuma a ranar an fi mayar da hankali ga jawabai a game da harkokin kasuwancin fim a kafafen sadarwa irin su YouTube, Instagram da kuma manyan gidajen talabijin da ake haska finafinai a duniya.

Baya ga haka an bayar da lokaci mai tsawo na yin tambayoyi ga mahalarta taron inda aka shafe tsawon sa’o’i uku ana tambayoyi tare da muhawara.

An dai kammala taron da misalin ƙarfe huɗu na yamma kuma da dama cikin mahalarta taron sun bayyana jin daɗin su da yadda taron ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Loading

Tags: GooglehoraswaKannywood
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai na so masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta su riƙa nuna Nijeriya da kyau

Next Post

Abin da ya sa na buɗe WikiHausa – Chamo

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Abin da ya sa na buɗe WikiHausa – Chamo

Abin da ya sa na buɗe WikiHausa - Chamo

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!