SHUGABAN gidan yanar WikiHausa, Alhaji Isa Uba Chamo, ya bayyana cewa ya ƙirƙiri manhajar ne domin ta samar da ingantaccen ilimi kan rayuwar Bahaushe a harshen Hausa a intanet.
Ya bayyana haka ne a taron ƙaddamar da manhajar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Gidan Mambayya da ke unguwar Gwammaja, Kano, a ranar Asabar.
Chamo ya ce aƙalla shekara shida kenan da kafa gidan yanar amma da yawan mutane ba su san shi ne ya ƙirƙire shi ba, wasu sun ɗauka ‘yan ƙasar waje ne suka yi ta.
Ya ce: “WikiHausa manhaja ce da muka ƙirƙira domin samar da kowane irin ilimi cikin harshen Hausa a yanar gizo wanda take kiyaye al’ada da addinin malam Bahaushe.
“Kuma ta ƙunshi komai domin muna da marubuta 1,800 daga faɗin duniya. Duk abin da aka turo mana za mu duba mu gyara sannan mu ɗora duniya ta gani.
“Ba iya Nijeriya ba ne ake sauraron mu ba, sama da ƙasashe ashirin suna bibiyar mu a duniya. Muna da mabiya da yawa a duniya.”

Tun da farko a jawabin sa, babban jigo a tafiyar, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana cewa WikiHausa tana ƙunshe da duk wani abu ingantacce na Bahaushe.
Ya ce ko da Hausa aka yi ko da Larabci aka yi ko da Turanci aka yi in dai a kan Hausa ne, to WikiHausa za ta saka shi.
Ya ƙara da cewa, “WikiHausa ba tana nufin harshen Hausa ba ne kawai, a’a ana maganar al’ummar Hausawa da kuma rayuwar Hausawa baki ɗaya.
“A baya Turawa suna zuwa bincike-binciken su a kan Hausawa, amma da matsalar Boko Haram ta zo sai suka tsorata suka daina zuwa. To daina zuwan su sai ya ba mu ƙwarin gwiwa, domin da suka daina zuwa sai muka zame masu hanyar da za mu riƙa ba su bayanan mu.
“Domin mu abin da muke so shi ne da ɗan Chaina ya zo ya yi bincike a kan Kasuwar Kantin Kwari, gara mu je mu kai masu. Wannan shi ne muhimmancin WikiHausa, kuma in-sha Allahu ba mu fara don mu daina ba.
“Duk da yake ‘yan’uwan mu ba sa so, amma muna da yara zarata kuma zafafa da suke taimaka mana, mu gyara shi ta yadda za a yi amfani da shi a duniya.”