A daren 27 ga Oktoba ne Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Oscar, ya sanar da ajiye muƙamin sa wanda ya shafe tsawon shekara guda akan muƙamin.
Kamar yadda ya sanar a shafin sa na Facebook, Sunusi Oscar ya wallafa cewa: “Wannan muƙami da aka bani A Wannan Gomnati NA S S A KANNYWOOD daga wannan rana irin ta yau na ajiye shi, kuma ina Godiya ga Allah.”
Sai dai babu wani ƙarin bayani da ya yi bayan wannan ɗan gajeran rubutun da ya yi.
Hakan ya sa muka kira wayar sa domin neman ƙarin bayani, amma dai bai ɗaga wayar ba.
![]()







