HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) tare da haɗin gwiwar reshen ta na Jihar Kebbi, ta karrama gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu), da lambar yabo.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar, Ibrahim Amarawa, ya rattaba wa hannu a yau, ta ce sun karrama gwamnan ne saboda ƙoƙarin sa na bai wa mawaƙa da ‘yan wasa da sauran masu harkar industiri mutum 100 muƙaman masu taimaka masa (Special Assistants, SA).
Amarawa ya ce, “Wannan lambar yabo da Kungiyar ta bayar har ila yau yana daga cikin kokarin da wannan shugabanci na MOPPAN yake yi domin fitowa da martabar ƙungiyar a idon shugabanni da al’umma.
Ya ce taron ya samu nasara domin shugabannin MOPPAN sun samu karɓuwa a Jihar Kebbi da kuma samun tabbacin ci gaba da hulɗa domin bunƙasa industiri.