HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta bayyana ƙudirin ta na shirya gayyatar dukkan ‘yan Kannywood zuwa wuri addu’ar bakwai na marigayiya Fatima Sa’id Abdullahi Yakasai (Bintu ‘Daɗin Kowa’).
Ta ce ta na gayyatar kowa da kowa.
Ƙungiyar ta ta fitar da takardar gayyatar ne a yau Juma’a, ɗauke da sa-hannun shugaban ta, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.
Ƙungiyar ta ce, “Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) reshen Jihar Kano, su na gayyatar ‘ya’yan wannan masana’anta ta Kannywood zuwa taron addu’ar kwana bakwai na rasuwar ‘yar’uwar mu Fatima Sa’id (Bintu ta ‘Daɗin Kowa’).”

Za a gudanar da taron a jibi Lahadi, a Social Welfare, Court Road, Kano, da misalin ƙarfe 3:00 na yamma.