A YAU Talata, 4 ga Afrilu, 2022 Allah ya ɗauki ran mahaifin fitattun ‘yan fim ɗin nan da ke garin Kaduna, wato Alh. Yusuf M. Gidaje, Sabi’u M. Gidaje, Haruna M. gidaje da Nafi’u M. Gidaje.
Alhaji Muhammad Gidaje, mamallakin kafanin ‘Gidaje Group’, ya rasu da misalin ƙarfe 1:30 na rana a gidan sa da ke Kwanar Lami Filato, Tudun Wada, Kaduna.
Marigayin ya rasu ya na da kimanin shekara 108 a duniya.
Ya bar matan sa na aure uku, ‘ya’ya 16 da kuma jikoki 121.
Kamar yadda ɗaya daga cikin ‘ya’yan sa ya shaida wa mujallar Fim, mahaifin nasu ya kai kimanin wata shida ya na jinya; ashe jinyar tafiya ce.

An sallaci gawar Alhaji Muhammad Gidaje a ƙofar gidan sa da misalin ƙarfe 4:15, daga nan kuma aka ɗauke shi zuwa gidan sa na gaskiya a tsohuwar maƙabarta da ke Titin Ɓachama, Tudun Wada.
A harabar wurin da aka binne marigayin ƙarƙashin wata bishiya, duk kewayen wurin ƙaburburan ‘ya’yan sa da jikokin sa ne; shi ne na 11 da aka binne a wurin, inji ɗan sa Alhaji Yusuf.
‘Yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Malam Murtala Aniya, Abdullahi Abu Uku, Abdul SD, Yahuza Ilu, Zaharaddin Mando da Isah Man United.
Mujallar Fim ta zanta da Alhaji Yusuf game da wannan babban rashi da aka yi masu, inda ya ce, “Alhamdu lillahi! Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Yau uku ga watan Ramadan, Allah ya yi Alhaji Muhammad Gidaje rasuwa, wanda shi ne mahaifin mu. Ya rasu ne sanadiyyar rashin lafiya da ba ta wuce ta ‘yan kwanaki ba.
“Alhamdu lillahi, Alhaji ya rasu a yadda ake so duk wani Musulmi ya rasu.
“Mu na godiya ga dukkan waɗanda su ka halarci jana’izar sa. Allah ya saka da alheri.
“Allah ya jiƙan shi da gafara, ya sada shi da mala’ikun rahama, ya kuma yaye masa ɗacin mutuwa.”
Game da abin da zai iya tunawa game da mahaifin su, Alhaji Yusuf ya ce, “Alhamdu illahi! Kullum in mu ka zauna da shi babu abin da ya ke ce mana sai mu riƙe amana; ‘in ku ka riƙe amana za ku ji daɗin rayuwar ku.’
“Haka kuma ya na yawan faɗa mana cewa mu kiyayi dukiyar jama’a. ‘Ku zauna da kowa lafiya.’

“Ya rage saura kwana uku zai rasu aka ce za a kai shi asibiti, sai ya ce, ‘A’a, ko an kai ni asibiti babu abin da za a iya yi, girma ne. Ku dai ci gaba da yi mani addu’a, in ta zo Allah ya sa mu cika da imani.’
“A haka ya ci gaba da kalmar shahada har Allah ya yi masa wa’adi, ya cika. Wannan ya sa na ke ta yi wa Allah godiya da addu’ar Allah ya sa mu ma mu samu damar tafiya ta yadda ya tafi.”
Alhaji Yusuf Gidaje furodusa ne, wanda shi ya gaji yayan sa marigayi Alhaji Alƙasim Gidaje, wanda ya shirya fim ɗin ‘Shahada’ a ƙarƙashin kamfanin su mai suna ‘Gidaje Film Production’.
Shi kuma Sabi’u ɗan wasa ne kuma furodusa. Sai Haruna, shi kuma darakta ne, sai autan ɗakin su Nafi’u shi kuma mawaƙi.
Allah ya jiƙan Alhaji Muhammadu Gidaje, ya albarkaci dukkan abin da ya bari, amin.
