JARUMAR Kannywood, Hadiza Kabara, ta nemi jama’a da su taya mata ‘yan fim da addu’ar Allah ya kawo masu mazajen aure.
Hadiza ta yi wannan roƙon ne a lokacin da take gabatar da nasiha ga ango da amarya a lokacin taron bikin auren A’isha Ibrahim Yusuf, ‘yar jaruma Asma’u Sani, wanda aka gudanar a ranar Juma’a a wurin taro na otal ɗin The Afficent da ke Sultan Road, Kano.
Tun da farko sai da jarumar ta yi nasiha ga ango da amarya inda ta ja hankalin su a kan su zauna lafiya, kuma su yi haƙuri da juna, domin shi zaman aure ɗan haƙuri ne.
Ta ce: “Mu iyaye ne a gare ku, don haka ina yi muku nasiha irin ta iyaye. Ku yi haƙuri, ku yi haƙuri, komai na duniya ɗan haƙuri ne, don haka ku ma ku rungumi haƙuri sai zaman ku ya yi kyau har a rinƙa alfahari da zaman ku kowa yana jin daɗi. Kowa zaman haƙuri yake yi.”
Da ta juya kan halin da jarumai mata suke ciki, sai ta ce: “A yanzu mu ma muna son aure. Kullum addu’ar mu kenan, Allah ya kawo mana mazajen aure.
“Mu mata ‘yan fim muna da buƙatar mu yi aure, don haka jama’a masoya ku taya mu da addu’a Allah ya kawo mana mazajen aure, don mu ma mu samu mu shiga daga ciki.
“Muna addu’ar Allah ya kawo mana mazajen aure nagari masu son mu da alheri.”