• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Murna ta cika Maryam Mushaqqa da mijin ta kan auren ‘yar su Illaf ran Asabar

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 26, 2022
in Ranar Murna
0
Illaf Muhamed Auwal

Illaf Muhamed Auwal

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MURNA ba ta misaltuwa a wajen tsohuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Aliyu Umar Ampi, a wannan makon saboda auren ɗiyar ta, Illaf, wanda za a ɗaura gobe Asabar, 27 ga Agusta, 2022.

Tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da Maryam Mushaqqa, ta auri Alhaji Muhamed Auwal Galadima ne a ƙasar Kamaru yau shekara 19, kuma auren ya yi albarkar ‘ya’ya da cigaban rayuwa.

Auren nasu babban misali ne na ‘yan fim masu yin aure su zauna, kuma ya karya lagon iƙirarin da wasu ke yi cewar wai ‘yan fim mata ba su zaman aure.

A tattaunawar da su ka yi da mujallar Fim a yau, Hajiya Maryam da Alhaji Auwal sun bayyana matuƙar murna kan wannan abin farin ciki da ya same su na aurar da babbar ‘yar su.

Amarya Illaf da ango Hassan Yuguda

Iyayen amaryar sun kuma yi tsokaci dangane da masu cewa ‘yan fim mata ba su zaman aure.

Mushaqqa ta ce: “Assalamu alaikum. Barkan mu da safiya, ina gaishe da kowa. Ina yi wa makaranta Fim Magazine fatan alkhairi. 

“Gaskiya ba zan iya misalta farin cikin da na ke ciki ba kasancewar ban saba ba, ban taɓa zaton zan yi tsawon rai har in ga wannan rana ba. So, ina cikin annashuwa da farin ciki, ina kuma addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya kaɗe masu fitina. Irin ni ma na yi suriki, ka gane irin abin! Abin na da daɗi sosai, kuma abin alfahari ne. 

“Allah ya sa mutu-ka-raba. Allah ya sa su yi dogon zango na rayuwa mai albarka, amin.

“Sai kuma godiya ta musamman ga maigida na da ya nuna mana ƙauna da kulawa. Allah ya saka masa da alkhairi. Allah ya sa ya gama lafiya, amin.   

“Ina kuma miƙa gaisuwa ta ga ƙawaye na na Nijeriya da nan da su ka goya min baya da addu’o’i da ƙarfin su da jikin su da bakunan su masu albarka. Ina godiya.”

A kan maganar auren ‘yan fim, mahaifiyar su Illaf ta ce: “Maganar ‘yan fim ba su zaman aure, majority waɗanda su ke karanta labarai ko kuma yanzu da abubuwa su ka yawaita, komai a bayyane ya ke, su kan su in za su yi adalci sun san ba haka ba ne, domin aure kamar rai ne da shi, idan Allah ya yi zai mutu, to duk yadda ka ke son sa sai ya mutu, sai an rabu. Don haka ina yi maku fatan alkhairi. Na gode sosai. 

“Sai kuma a taya mu da addu’a, Ubangiji Allah ya kawo na ‘yan baya. Dukkan ‘yan’uwa Musulmai da su ke zaune a gidajen su Allah ya ƙara masu haƙuri da zaman lafiya, waɗanda kuma ba su da gidaje – zawarawa da ‘yan matan mu – Allah ka ba su masu riƙe su bisa gaskiya. Na gode.”

A nasa ɓangaren, shi ma Alhaji Auwal ya tofa albarkacin bakin sa a kan maganar wai ‘yan fim mata ba su son zaman aure, ya ce, “A gaskiya wannan maganar ba gaskiya ba ne. Shi aure ko a Madina ma ana iya rabuwa, kuma ko wace mace da irin halin ta.

Gobe ce ranar ta! Amarya Illaf

“Yau shekarar mu goma sha tara mu na tare lafiya lau. Kuma ban da ita akwai da yawa daga cikin ‘yan fim da su ke zaune a gidan aure lafiya lau. Kowace mace ta na da irin tarbiyyar da iyayen ta su ka ba ta.”

A gobe Asabar, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, za a ɗaura auren Illaf Muhamed Auwal Galadima da angon ta, Hassan Yuguda, a garin Douala na ƙasar Kamaru.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Mahaifiyar amarya, Hajiya Maryam, tare da ƙanwar mahaifin amarya
Biki ya kankama!
Hassan Yuguda da amarya Illaf Muhamed Auwal

Loading

Tags: aureDoualaIllaf Muhamed AuwaljarumaKamaruKannywoodMaryam Aliyu Umar AmpiMaryam MushaqqaMuhamed Auwal Galadima
Previous Post

Rarara baba na ne, inji Maishadda

Next Post

Hukumar Hisbah ta goyi bayan manufofin ƙungiyar mata ‘yan fim

Related Posts

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar
Ranar Murna

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar

July 22, 2025
Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu

July 18, 2025
Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

July 16, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Next Post
Mata 'yan fim daga ƙungiyar AKAFA a ofishin Kwamandan Hisbah, Ustaz Haruna Sani Ibn Sina

Hukumar Hisbah ta goyi bayan manufofin ƙungiyar mata 'yan fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!