• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mutuwar Kamal Aboki darasi ce a gare mu, inji jarumin Kannywood BMB

by DAGA ABBA MUHAMMAD
January 19, 2023
in Labarai
2
Marigayi Kamal Aboki

Marigayi Kamal Aboki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI kuma darakta a Kannywood, Bello Muhammad Bello (General BMB) ya yi magana cikin alhini a game da irin abubuwan da matashin jarumin barkwanci Kamilu Iliyasu Usman, wanda aka fi sani da Kamal Aboki, ya ke yaɗawa na alkhairi a soshiyal midiya kafin rasuwar sa, saɓanin irin abubuwan da wasu ke yaɗawa.

BMB ya ɗora bidiyo a Instagram, sannan a jikin bidiyon ya rubuta Kamal Aboki zai girbi abin da ya shuka.

Ya fara da cewa, “Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu. To, kullum ga shi maganar da mu ke faɗa wa mutane ba su so su yi amfani da shi, wasu na ganin cewa idan an yi magana a’a, idan ka yi abu na kirki ko bayan ba ka nan mutane shi za su kalla su yi magana, in ka yi ba na kirki ba ko da kaɗan ne za a yaɗa a riƙa magana a kan ka. 

“Yanzu ku duba fa, saboda Allah fa Kamal Aboki ga shi Allah ya ɗauki ran shi ba ya duniya, ga shi kuma ya yi wasu abubuwa, ni fa zan nuna a bidiyos ɗin zan nuna a gaba saboda ya zama darasi. Na san wasu za su ji haushi, amma sai na nuna. 

“Ya na can, ga shi ba ya nan, kuma lallai lallai sai ya tarar da ‘result’ abin da ya yi, musamman a wannan bidiyos da zan nuna maku.

“Kawai abin da zan ce Allah ya jiƙan Musulmi, shi ne kawai. Amma wallahi ba zan yi kuka ba.”

Bidiyoyin da BMB ya nuna, an nuna Kamal ya na magana a kan mai kuɗin da ba ya zakka, ba ya taimako, ɗayan kuma a kan talakan da ba ya sallah, ba ya salati, ba ya addu’a.

Bayan nuna bidiyoyin, sai BMB ya ci gaba da cewa, ” Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Yanzu saboda Allah a duk sana’ar da za ka yi a duniya ba wai haramun ba ne. Yanzu wannan bawan Allah  da wannan abin kawai ya tsira a rayuwar sa, ya bar abubuwan da duk wanda ya gani zai yi masa addu’a. Irin komedin da ya ke yi kenan, babu batsa, babu wani abu, sai dai abu a hikimance. 

“Kai, Allah ya jiƙan shi, Allah ya gafarta mashi, mu kuma Allah ya kyauta ƙarshen, ya sa mu gama da duniya lafiya. Amma duniya ba matabbata ba ce.”

A nasa ɓangaren kuma, wani matashin ɗan jarida mai suna Kwamared Abba Sani Pantami, shawara ya ba ‘yan’uwan marigayin a Facebook, inda ya ce, “Ina ba wa ‘yan’uwan marigayi Kamal shawara, don Allah su daure su goge shafukan shi na Facebook, Tiktok, Instagram, YouTube da sauran kafofin sada zumunta da ya ke da alaƙa da su.”

Abba ya ci gaba da cewa, “Hakika Kamal ya samu kyakkyawar shaida a wurin dubunnan mutanen da ya ke mu’amala da su. Hakan abin farin ciki ne babba kuma kowa ya na burin samun kyakkyawar shaida a lokacin da ya koma ga mahaliccin shi.”

Wataƙila wayar shi ta shiga hannun ‘yan’uwan shi, ina mai roƙon su don Allah da su taimaka su goge dukkannin shafukan shi da YouTube Channel ɗin shi saboda wasu ‘yan dalilai kamar haka:

General BMB (a hagu) da kuma Abbas Sani Pantami

“Na farko a wannan lokacin mutane da dama su ka fara sanin wanene shi, wasu da dama su na ta shiga shafukan shi na Facebook, TikTok, Instagram da YouTube da sauran su, domin ganin bidiyoyin da ya yi na tsawon shekaru wanda duk wani mai son shi da gaske ba zai so hakan ba. 

“Abu na biyu matuƙar aka yi ƙoƙarin goge shafukan shi na tabbata bidiyon shi da dama za su ɓata, ba za a sake ganin su ba, madadin ba a goge shafukan ba.

“Abu na uku, mun san da cewa ko da kuskure guda mutum ya yi a duniya, bai kamata bayan mutuwar shi a riƙa ganin kuskuren har ana tunawa da shi ba da sauran wasu dalilai wanda ba sai na zayyano su ba.

“Don Allah, don Allah, don Allah ina mai roƙon makusantan shi da su taimaka su yi aiki da wannan shawarar tawa. 

“Hakika Kamal Aboki ya na ɗaya daga cikin matasan da su ke burge ni, musamman a ɓangaren nishaɗantarwa. Ina matuƙar ƙaunar shi, shi ya sa na ke ba wa ‘yan’uwan shi wannan shawarar, ina fatan kuma za ku fahimce ni. 

“Allah ya jiƙan Kamal, mu ma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani ya hayyu ya ƙayyum.”

Loading

Tags: Abbas Sani PantamibarkwancibidiyoyiGeneral BMBKamal Abokimutuwarasuwasoshiyal midiya
Previous Post

Zaɓen 2023: Atiku ya sha alwashin ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarfin iko

Next Post

Abale zai angwance a mako mai zuwa

Related Posts

Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Next Post
Katin gayyatar ɗaurin auren Abale

Abale zai angwance a mako mai zuwa

Comments 2

  1. Mohammed kawu ceto says:
    3 years ago

    Allah yajikansa da rahama

  2. Mohammed kawu ceto says:
    3 years ago

    Comment: allah yajikansa da rahama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!