AN bayyana cewa samun muƙami da jarumi Ali Nuhu ya yi a gwamnatin Tinubu wata dama ce Kannywood ta samu wadda bai kamata a bari ta suɓuce ba tare da an ci moriyar ta ba.
Babban furodusa kuma jigo a Kannywood, Alhaji Abdulkareem Mohammed, shi ne ya faɗi haka a daren jiya Litinin a wurin gagarumar dinar taya murna da ‘yan Kannywood su ka shirya wa Ali Nuhu a Kano.
An yi liyafar ne don taya Ali murnar samun matsayin Manajan Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation, NFC) a otal ɗin The Afficent da ke Titin Magajin Rumfa a unguwar Nassarawa GRA, a Kano.
Tun da farko da ta ke jawabin maraba a wajen, shugabar kwamitin shirye-shiryen tsara taron, tsohuwar jaruma Hajiya Hindatu Bashir, ta nuna matuƙar farin cikin ta kan yadda ɗimbin jama’a su ka halarci taron.
Ta ce, “Wannan taro da mu ka shirya, zan iya cewa shi ne taron da ya fi burge ni saboda ɗimbin jama’ar da su ka taru a wannan waje, domin kuwa wannan haɗuwa ce d

a ta zama ta tarihi a wannan masana’anta, saboda akwai fuskokin da su ka haɗu a wannan waje wanda rabon da a ga juna an shafe sama da shekaru ashirin, sai yau a wannan waje da Allah ya haɗa mu domin taya ɗan’uwan mu Ali Nuhu samun wannan muƙami da ya yi.”

Hindatu ta ƙara da cewa, “Babu shakka, Ali Nuhu wani jarumi ne na daban, domin kuwa yadda ya zauna da mutane lafiya da kuma yadda ya gudanar da tsarin rayuwar sa a ciki da wajen harkar fim ita ta kai shi samun matsayin nan, kuma ita ce ta kai shi ga haɗa wannan jama’a mu ka taru don mu taya shi murna, duk kuwa da cewa wannan matsayi ba nasa ba ne shi kaɗai, na dukkan ‘yan fim ne.
“Don haka mu na alfahari da Ali Nuhu. Mu na alfahari da wannan matsayi. Kuma za mu ba shi dukkan wani goyon baya da zai kai ga samun nasara a kan aikin.
“Mu na fatan Allah ya ba mu nasara, ya yi masa jagora.
“Yadda aka haɗu domin taya shi murna, Allah ya sa mu haɗu mu taya shi murnar ya kammala lafiya.”

Shi kuma a nasa jawabin, babban furodusa Abdul Amart Mohammed, wanda ya yi uwa da makarɓiya don ganin an tabbatar da taron, ya yi jawabi ne a game da dalilin da ya sa aka bai wa Ali wannan matsayin.
Ya ce, “Babu shakka, Ali Nuhu ya cancanci a ba shi wannan matsayi domin saboda abubuwa da dama da ya ke da su.
“Domin baya ga ilimin sa da gogewar da ta kai ga samun matsayin, haka nan Ali Nuhu ya kasance ɗan jam’iyyar APC da ta ke da gwamnati a tarayya, don haka duba da yadda mu ‘yan Kannywood mu ka bayar da gudunmawar mu wajen samuwar wannan gwamnati, tun a yaƙin neman zaɓe aka yi mana alƙawarin idan aka yi nasara za mu samu wani muƙamin da za a samu.
“To, idan ku ka duba, Ali Nuhu ya na cikin tsarin tafiyar APC wanda bai taɓa rawa ba; duk wani shige da fice da mu ka rinƙa yi na yaƙin neman zaɓe duk da shi mu ka rinƙa yi. Don haka ya ba da lokacin sa da jikin sa har ma da kuɗin sa don samun masarar APC.

“Don haka ko da mu ka ji sunan Ali Nuhu ya fito a matsayin wanda aka ba shugabancin wannan hukuma, wannan abin bai ba mu mamaki ba, saboda ya cancanta.
“Don haka mu na murna, mu na alfahari, za kuma mu ba shi goyon baya domin gudanar da aikin sa yadda ya kamata, domin mu na da ƙwarin gwiwar ba zai ba mu kunya ba.”
Shi kuwa a nasa jawabin, jigo a Kannywood, Malam Abdulkareem Muhammad, wanda ya yi jawabi a game da aikin Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya, cewa ya yi: “Ita wannan hukumar ta bunƙasa harkar fim ta ƙasa, aikin ta shi ne bunƙasa harkar fim da cigaban ta, wanda ya haɗa da samar da ayyukan fim ɗin ta hanyoyi da dama a ciki da wajen ƙasar da kuma wayar da kai a kan abin da ya shafi kasuwancin fim, da kuma wasu abubuwa da dama da ma’aikatar ta ke gudanarwa don bunƙasa harkar ta fim.
“To, da yake a yanzu wanda ya samu shugabancin wannan hukumar ɗan cikin mu ne, sai mu ɗauke ta matsayin tamu ce, kuma sai mu yi ƙoƙarin samar da duk wasu hanyoyin da za mu ci gajiyar ta yadda ya kamata.
“Don haka kada mu bari wannan dama da mu ka samu ta wuce mu.”
Alhaji Abdulkareem ya ƙara da cewa: “A yanzu masana’antar mu ta na buƙatar ilimi da kuma wayewa a kan kasuwancin fim a duniya wanda mu ke da ƙarancin sanin sa. Don haka babban abin da ya kamata mu yi a yanzu shi ne mu bai wa shugaban ta, Ali Nuhu, goyon bayan da zai samar mana da wannan cigaba, kuma mu na fatan za mu samu hakan daga gare shi.”
Bayan ya kammala jawabin ne aka shiga fagen nishaɗi inda aka saurari waƙar ‘Sangaya’ daga Misbahu M. Ahmad yayin da Fati Mohammed da Teemah Makamashi su ka yi masa amshi.
A lokacin dai an bi tsari da kuma dokar ƙasa ta haramta yin liƙi da kuma taka takardun naira, don haka aka ce duk waƙar da za a yi ba a yarda wani ya tashi ya yi liƙi ba. Hakan ya sa abin ya tafi cikin tsari ana hangen masu waƙar daga ko’ina a cikin ɗakin taron.
Bayan sun gama, sai ita ma Fati Nijar ta shiga fage ta yi waƙar ta ta ‘Carafke’.
Sannan Yakubu Muhammad da Sadi Sidi Sharifai su ka shiga su ka yi waƙoƙin su na baya.
Haka dai taron ya ci gaba da tafiya har tsakar dare, inda daga ƙarshe Ali Nuhu ya yi jawabin godiya.
A jawabin, ya gode wa dukkan waɗanda su ka bayar da gudunmawar su don samun matsayin da wanda su ka taya shi murna ta hanyar bayar da lokacin su da kuɗin su don ganin an shirya taron tare da dukkan mutanen da su ka halarci wajen.
Ya ce: “Ina yi wa kowa fatan alheri, da fatan komawa gida lafiya.”
Taron wanda aka fara da misalin karfe 9 na dare, ya samu halartar ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan kama daga ‘yan fim zuwa ‘yan kasuwa, sarakuna, ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati.