• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, May 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

by MUKHTAR YAKUBU
December 25, 2024
in Taurari
0
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

Fa'iza Abdullahi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood, Fa’iza Abdullahi, wadda aka fi sani da Bilki a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa 24, ta bayyana irin jin daɗin da take yi a duk lokacin da ta fito a matsayin masifaffiya a cikin fim.

Jarumar, wadda ke fitowa a matsayin matar Kofur Audu a shirin, ta bayyana haka ne ga mujallar Fim a lokacin tattaunawar ta da wakilin mu.

FIM: Mu fara da jin tarihin rayuwar ki.

FA’IZA: Na farko, suna na Fa’iza Abdullahi. An haife ni ne a cikin Jihar Bauchi, a wani gari da ake kira Jalaf a Ƙaramar Hukumar Damban. A can na yi karatu na girma duk a can.

A yanzu dai ban wuce shekara 26 ba, sai kuma a yanzu da na kasance a garin Kano ina gudanar da sana’a ta ta aikin fim.

Fa’iza Abdullahi

FIM: Shin fim ne ya kawo ki Kano kuma a wane lokacin kika zo?

FA’IZA: To gaskiya, zuwa na Kano zai kai shekara bakwai a yanzu kuma harkar fim ce ta kawo ni Kano, don in ban da ta dalilin fim ban san kowa a Kano ba, ban ma taɓa zuwa ba sai ta sanadin zan yi fim.

FIM: Da yake an fi sanin Fa’iza Abdullahi a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin matar Kofur Audu, ko kin taɓa yin wani fim ɗin kafin ki fara ‘Daɗin Kowa’?

FA’IZA: Gaskiya ban taɓa yin wani fim ba sai ‘Daɗin Kowa’, don da shi na fara. Ba zan manta ba lokacin da na zo garin Kano haka, ina zuwa Zoo Road akwai wani da na sani wanda shi ne darakta a fim ɗin a lokacin, nakan je na gaishe su, duk da ban ma san shi waye ba a lokacin, sai wata rana ya kira ni ya ce na zo ana nema na zan yi sin ɗaya a wani aiki, to ban ma san yadda abin yake ba sai da na je. To da haka na fara, har aka zo daga baya ake kira na lokaci zuwa lokaci.

Kuma lokacin da na fara fitowa a cikin ‘Daɗin Kowa’, a matsayin ‘yar tuwo-tuwo ce mai sayar da abinci, kuma ba mu da gida, ni kaɗai ce a wajen abinci sai masu zuwa su saya.

FIM: Shin akwai bambanci tsakanin rayuwar Fa’iza Abdullahi ta zahiri da kuma ta shirin ‘Daɗin Kowa’?

FA’IZA: To akwai bambanci sosai, saboda ka ga dai ita Fa’iza Abdullahi a zahiri ba ta faɗa, sannan tana girmama na gaba da ita da sauran abubuwa na girmamawa. Amma ita Bilkisu a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ ba ta da kunya, ba mu’amala mai kyau, ko gidan su ma ba ta girmama su ba. Haka gidan mijin ta ma ba ta raga wa kowa ba.

To amma sai ya kasance mutane a gari suna kallo na a matsayin Bilkisu maimakon su kalle ni a matsayin Fa’iza Abdullahi. Da yawa abin da na fi fuskanta a rol ɗin da nake, sai mutane idan mun haɗu su rinƙa cewa Allah ya ƙara. Abin da nake yi wa Kofur Audu suna jin daɗi saboda macuci ne azzalumi. Wasu kuma suna cewa bai kamata ba, na rinƙa sassauta masa.

Fa’iza Abdullahi: “An ba ni damar yin masifa”

FIM: Wane rol kika fi so a saka ki?

FA’IZA: Gaskiya duk da a cikin fim babu rol ɗin da ba na takawa, na fi so a saka ni na fito a masifaffiyar mace. Ina son na fito na yi masifa yadda rai na yake so. Don ka ga ko rol ɗin da nake yi a yanzu a cikin fim ɗin ‘Muhalli’ wani rol ne da na fito a matsayin matar aure amma marar mutunci, masifaffiya.

Don haka ina son rol ɗin sosai na fito a matar aure marar mutunci, marar tarbiyya. Don haka nake son rol ɗin, don an ba ni dama ina yin masifa yadda rai na yake so, kuma ga ni matar mai kuɗi, ina jin daɗin rayuwa, ga kuma ina zuba masifa. Don haka ina jin daɗi sosai da wannan rol ɗin.

Loading

Tags: Arewa 24Daɗin KowaFa'iza Abdullahi
Previous Post

Zaɓen MOPPAN 2025: Zazzagawa biyu, Cashman da Ability, za su kara a takarar shugabanci 

Next Post

Kalaman Shugaban Sojin ƙasar Nijar kan Nijeriya ƙage ne, cewar Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Ahmad Muhammad Umar (D. Prince)
Taurari

Gwagwarmayar jarumi, mawaƙi Ahmad D. Prince a Kannywood

April 20, 2023
Next Post
Kalaman Shugaban Sojin ƙasar Nijar kan Nijeriya ƙage ne, cewar Gwamnatin Tarayya

Kalaman Shugaban Sojin ƙasar Nijar kan Nijeriya ƙage ne, cewar Gwamnatin Tarayya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!