• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

by ABBA ILIYASU IBRAHIM TSANYAWA
May 13, 2024
in Mawaƙa
0
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

Rarara da Fatima wadda ya waƙe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WAƘA: ‘Fatima Mai Zogale’
MAWAƘI: Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara
MAI NAZARI: Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa, B.A. (BUK)

Gabatarwa

Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ da ta ja hankali a arewacin Nijeriya yanzu kuma ta samu shiga fagen nazari, inda wani marubuci kuma mai nazarin adabin baka Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa ya feɗe waƙar.

Kwarjini da karɓuwa da kuma daɗin waƙar da salon ta ake ganin ya ja hankalin mutane, musamman matasa (maza da mata) da dattawa da sauran masu sha’awar harkokin adabin Hausa wajen tofa albarkacin bakin su a kan waƙar, a daidai lokacin da ake cikin yanayin zaman tsadar rayuwa a ƙasar tare da matsalar ƙarancin man fetur. An kalli waƙar a matsayin wata abu da ta rage raɗaɗi tare da faranta wa al’umma rai, kamar dai yadda batun ta ya karaɗe kafafen sadarwar zamani, musamman na arewacin Nijeriya.

Ana nazarin waƙa ne a fagen ilimi idan ta dace da nazari da kuma abubuwan da nazari yake nema. Wannan ne dalilin da ya ja hankalin manazarcin waƙoƙin ganin ya nazarci waƙar ‘Fatima Mai Zogale’, don kuwa waƙar ta dace da nazari.

Rarara ya saki tallar waƙar ne a cikin ƙarshen watan Afrilu na shekarar 2024, inda ya saki cikakkiyar waƙar a farkon watan Mayu na shekarar, kuma sai ga shi ta samu karɓuwa nan da nan, musamman a kafafen sadarwa na zamani.

Fatima Mai Zogale

Yadda manazarcin ya feɗe waƙar
Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ tana da yawan ɗiya aƙalla guda 33. Waƙar ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin Hausawa mazauna mabambantan ƙasashen duniya, da sauran masu sha’awar harkokin Adabin Hausawa.
Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya rera waƙar ne da harshen Hausa, cikin karin harshen Kananci, duk da an samu tasirin karin harshen Katsinanci a ciki.

Mutane sun ƙaunaci waƙar wasu domin tausaya wa Fatima bisa korar ta da uwar ɗakin ta ta yi, wasu kuma don ganin a karon farko mawaƙin ya yi waƙa ga talaka (mai sana’a), wasu kuma saboda ƙaunar mawaƙin da kuma kasancewar ba kasafai yake waƙoƙin da ba na siyasa ba. A don haka aka yi ta hawa waƙar, a kwana biyu ta karaɗe arewacin Nijeriya. Waƙar ta zamo waƙa ta uku a waƙoƙin da ke tashe a arewacin Nijeriya, daga bisani ta zamo waƙa ta ɗaya kamar yadda binciken masana ya nuna.

Tarihin Mawaƙi

Alhaji Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, an haife shi ne a Jihar Katsina, a ƙauyen Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja, a ranar 13 ga Satumba, 1986. Shahararren mawaƙin ‘yan siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi a fannin rera waƙoƙi musamman na ‘yan siyasa da sarakuna, kuma mai hasashen abubuwan da ka iya zuwa su zo.

Duk da cewa ya taso a garin Kano domin neman Ilimin Alƙur’ani, ya shiga hidimar waƙa ne aƙalla shekaru ashirin da suka gabata. A yanzu a Facebook kaɗai yana da mabiya fiye da miliyan ɗaya, ga kuma YouTube da Instagram da TikTok da X (Tweeter a da) da makamantan su.

Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara)

Wasu Dalilai Na Amsuwar Waƙar

1. Amsuwar waƙa yana da tasiri da sanuwa ko shura na mawaƙi, kasancewar Alhaji Dauda mawaƙin da furar shi ke kan dawo, kuma mai tarin mabiya ya ƙara taimakawa wajen amsuwar waƙar a ɗan ƙanƙanen lokaci.
2. Al’umma suna wani yanayi na ƙarancin man fetur, saboda haka zirga-zirga ta taƙaita, akwai lokacin sauraren abubuwa, kuma lokaci ne na buƙatar nishaɗi domin rage raɗaɗin matsalar mai da tsadar rayuwa.

3. Ba a saba jin Alhaji Dauda yana waƙa ga wani mai ƙaramin ƙarfi ba, sai ga shi a karon farko yana waƙa ga wadda ba tabbacin a same ta da naira dubu ashirin ta kan ta.
4. Babban dalili kuma shi ne matakin da uwar ɗakin Fatima ta ɗauka na korar ta daga aiki, ya ɗauki hankalin mutane wajen bibiyar al’amarin don ganin sakamakon da Fatima za ta samu, musamman daga wanda ya yi mata waƙar.

2.0 Saƙo Ko Turken Waƙar

2.1 Gundarin Turke
Babban saƙon da wannan waƙa ta ke ƙunshe da shi, shi ne zuga tare da yabawa da kwarzantawa da nuna gamsuwa bisa sana’ar Fatima ta sayar da zogale, kenan jigon ta yabo ne.

Mawaƙin ya yi ƙoƙari matuƙa wajen fitar da turken waƙar da ma ƙananan tubalai tun daga ɗan waƙar na farko har zuwa na ƙarshe.

Mawaƙin ya nuna ƙwarewa wajen ƙulla waƙar da ƙafiyoyi na ciki da na waje.
Ya nuna ƙwarewa wajen zaɓo kalmomin zuga da yabo da kwarzantawa a lokacin ƙulla waƙar, wanda hakan ya ƙara wa waƙar armashi da daɗi.

2.2 Muhallan Turken Waƙar:

A wasu misalai na muhallan turke na wannan waƙa su ne inda ɗa na 7 da ɗa na 5 suke faɗin:

Jagora: Na yaba mai zogalen garin nan na gudu ban tsira ba
: Fati masu kwaɗon zogalen mu ran nan ta yi murace
: Fati Fatima kenan aradu zancen Fatima bai ɓuya ba
: Kyau da diri naki zan kwatance ba ɗan ganin ki ba
: Kyakkyawa ta fito ku layu

2.3 Taƙaita Turken Waƙar
Saƙonnin da wannan waƙa ta ƙunsa a gunduwa-gunduwa ta ma’ana sun haɗa da:

  • Ɗa na 1-5: suna wasa wadda ake yi wa waƙa cikin salon na zuga da kambama da yabawa.
    Ɗa na 6: bayyana muhallin turken waƙa, wato jigon waƙar.
  • Ɗa na 7-15: yabo tare da wasu shawarwari ga rayuwar Fatima a kan sana’ar ta da kuma abubuwan da ka iya zuwa su zo.
    Ɗa na 16-19: habaici ga maƙiyan Fatima, tare da ƙara tabbatar da asalin Fatima da ƙara mata shawarwarin jan hali da tattali, da kuma rabuwa da maƙiyan ta, wato kada ta tanka masu.
  • Ɗa na 20-22: bayyana wasu siffofin wadda ake wa waƙa, mai ‘yar gira a goshi, mai kwale, tare da shawarwarin ta ƙara riƙe masoyan ta hannu biyu, ta kuma yi watsi da maƙiyan ta.
  • Ɗa 23-26: shawarwari ne a kan Fatima ta riƙe sana’ar ta hannu bibbiyu, kada ta yarda da bashi, kowa ya miƙa kuɗin shi ta ba shi zogale, kowa ya taho sayen zogale ta jira shi, saboda kula da abokan kasuwa.
  • Ɗa na 27-30: ƙara yaba siffar Fatima, musamman kyau da dirin ta tare da faɗo wasu kyawawan halayen ta irin na taimakon marayu, da ku ma yadda take goya mabuƙata.
  • Ɗa na 31-33: jaddada yabon Fatima tare da kira a gare ta da ta ɗauki shawarwari da bayanan da aka zayyana a waƙe, wato kyan koyarwar ƙwarai a koyu.
Fatima a wurin sana’ar ta ta zogale

3.0 Awon Baka Na Waƙar

Yawan layuka na ɗa

Zubin ɗiya a waƙar:

An buɗe waƙar ne da kiɗa na kayan kiɗan situdiyo, wato gangunan Turawa, sannan aka ci gaba kai-tsaye da zuba ɗiyan waƙar.

Tsarin ɗa ko ɗiya a waƙar

Tsarin Rerawa

Takidi a ɗiyan waƙar

Karin murya da amsa amon waƙar

4.0 Adonta Harshe A Waƙar

Alamtarwa = Kalmar Adon gari (ɗa na 24)

Kamantawa = ɗa na 19

Siffantawa = ɗa na 28, da ɗa na 29, da 20: Fatima ga ɗan kwalen ta ga shi

5.0 Aiwatar Da Harshen Waƙar

Yawan kalmomin waƙa = waƙar na da kalmomi 605

Zaɓen kalmomi = Misali ado, gira, dila, kandala, gudu, labule, ilimi, dangwale, dunƙule, zogale, tsira, bakin uwa, tattali, sangali, marayu, taimako, birni

Karin Magana: kwalli dai na ido ne: ɗa na 11.
Kyauta ta yi kamar tsintuwa : ɗa na 10
Karin harshe na waƙar = Kananci

Ginin jumla a waƙar = Akwai nau’o’i daban-dabam, kamar:

Jumla Sassauƙa: ɗa na 1, ɗa na 17 da 19 da ɗa na 29

Jumla Tsattsaura: da na 19, ɗa na 11.

Jumla umartau: ɗa na 14, ɗa na 17, ɗa na 18 da na 21.

Jumlar Aikatau: ɗa na 23, ɗa na 24

6.0 Tasirin Waƙar Ga Al’ummar Hausawa

Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ waƙa ce da ta fito a lokacin da ake da ƙishirwar wata waƙa irin ta wadda za ta samar da farin ciki tare da rage raɗaɗin da al’umma suke ciki. Waƙar ta amsu kuma ta yi tashe, mutane sun amshi waƙar ka’in da na’in, inda suka yi ta hawan ta a kafafen sada zumunta musamman kafar TikTok da Facebook.

Waƙar ta dace da sharuɗɗan da masana suka gindaya na nazarin waƙar baka Bahaushiya, kuma ta dace da kyawawan al’adun Hausawa, ba ta saɓa da koyarwar addinin Musulunci ba, don kuwa a nazarin ta da aka yi ba a samu munana ko ɓatanci ga al’ada da addini ba, ba a samu maganganun tayar da sha’awa ko batsa a cikin ta ba, sai ma ƙoƙarin taskace al’adu da tsofaffin kalmomi a cikin ta. Don haka waƙar ba ballagaza ba ce, waƙa ce da za a ƙarfafi mutane da su saurara kuma su nazarta.

Ɓangaren sana’a kuwa, waƙar ta ƙara fito da mutuncin sana’ar Hausawa ko a ce abincin Hausawa, wato zogale, don kuwa wasu alƙaluman bincike sun nuna yadda al’umma suka ƙara ƙaunar zogalen.

* Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa, B.A (BUK), marubuci ne, mai sha’awar harkokin adabi da al’adun Hausawa
08037672040 Imel: Comr.abbatsanyawa@gmail.com

Loading

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaFatima Mai Zogalenazarizogale
Previous Post

An samu nasarar yi wa Maryam Waziri tiyata a fuska

Next Post

Abin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin tallafa wa tsaron yanar gizo – Minista

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita
Mawaƙa

Ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ba ta siyasa ba ce, inji Ali Isah Jita

December 3, 2023
Next Post
Duk da matsalolin da ake ciki, Nijeriya za ta ci gaba da bunƙasa – Minista Idris

Abin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin tallafa wa tsaron yanar gizo - Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!