AN samu nasarar yi wa tsohuwar Kannywood Maryam Waziri tiyata a fuskar ta sakamakon damejin da fuskar ta yi a mummunan haɗarin mota da ya ritsa da su a Zariya.
Maryam da mijin ta, fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa Tijjani Babangida, da ɗan su Fadeel, da ƙanen Tijjani wato Ibrahim Babangida da kuma ‘yar aikin su sun yi haɗarin ne a unguwar Ɗanmagaji a Zariya shekaranjiya.
Ibrahim ya rasu nan take, yayin da Fadeel ya rasu a lokacin da ake masa tiyata a daren jiya.
A yau hoton damejin da fuskar Maryam ta yi ya watsu a soshiyal midiya.

An yi mata tiyata a ƙarƙashin jagorancin Dakta Abubakar Gumi na Asibitin Koyarwa na Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya.
Kamar yadda abokin Tijjani, Alhaji Bala Ɗanjuma Yaro, ya bayyana a Facebook, ya ce, “Ina tare da Tijjani awa biyu bayan haɗarin har zuwa ƙarfe 10:00 na dare. Haka yau ma ina tare da shi a Zariya.
“A wannan lokacin na ziyarci Maryam Waziri a ICU. Sannan mu ka tuƙo mota da Tijjani daga Zariya zuwa Kaduna kafin ya wuce Abuja ‘yan mintoci da su ka wuce.”
Bala ya ci gaba da cewa, “Tijjani Babangida ya samu sauƙi cikin hankalin sa, sai dai ‘yan raunuka da ya samu. Yanzu kuma ya na kan hanyar sa ta zuwa Abuja saboda ci gaba da duba lafiyar sa.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ɗazu da rana an yaɗa ji-ta-ji-tar cewa Maryam ta rasu, wanda ba gaskiya ba ne, wasu ne su ka ƙirƙiri labarin su ka yaɗa.