LOKACIN da ya shigo industiri, ya shigo ne da buri biyu, wato ya zama jarumin fim da kuma rera waƙa. Da ya ke sa’ar sa ba a fim ɗin ta ke ba, sai Allah ya ba shi luɗufi a ɓangaren waƙa. Sannu a hankali ya ƙware, yanzu haka ya na ɗaya daga cikin matasan mawaƙan da ke ƙarƙashin fasihin mawaƙin nan, Aminu Alan Waƙa.
Baya ga sana’ar waƙa, Usman, wanda aka fi sani da laƙabin Shehu Shaga a fagen waƙa, ya ƙware a kan sana’ar ɗinki. Tela ne wanda ya karɓu ga manyan mutane, amma rayuwar sa ta fi raja’a a kan harkar waƙa. Me ya sa? Menene labarin sa? Yaushe ya shiga harkar? Ko ya fara cin ribar ta? Ya aka yi ya haɗu da Ala? Shaga ya ba da amsoshin dukkan waɗannan tambayoyin a tattaunawar da ya yi da mujallar Fim.
Da farko cewa ya yi, “Suna na Usman Yusuf. An haife ni a Zariya ne a shekarar 1982, kuma a nan na yi firamare. Sannan na fara sakandare a Soba, daga bisani na ƙarasa a Kwalejin Tunawa Da Sardauna da ke nan Kaduna.
“Mahaifi na ɗan asalin garin Saminaka ne, mahaifiya ta kuma Bafillatanar Gombe ce.”

Bari mu ji yadda ya tsinci kan sa a harkar fim. “Wato tun farko akwai wani wa na ana ce masa Muhadda Yahaya, wanda sun yi wasan kwaikwayo da su Ƙasimu Yero. Ba ni mantawa, lokacin ina ɗan ƙaramin yaro, akwai wani wasan bidiyo da su ka saka ni a ciki. To shi wan nawa a lokacin ya na a garin Kontagora. Sai su ka ƙirƙiro wata ƙungiyar wasan kwaikwayo, kuma shi ne shugaba. Ta dalilin su ne ‘yan fim su ka fara shiga wajen su na ɗaukar fim. To na kan je kallo, sai abin ya shiga rai na ƙwarai, na ji ina sha’awar in shiga a yi da ni. Har marigayi Ahmed S. Nuhu ya taɓa gayyata ta ya ce in shigo mana a riƙa saka ni a fim.
“To ni kuma a wancan lokacin ina makaranta, kuma ba ni so in samu matsala da ita. To bayan na kammala makarantar sai na tafi Kano. Da na je sai na sauka a gidan su Ala. Lokacin akwai wani yayan sa, wanda tela ne, ana kiran sa Nasiru. Na same shi, a hankali mu ka kama harkar ɗinki tare. A lokacin ma shi Aminu Ala bai fara waƙa ba, rubutun littattafai ya ke yi, wato shekarar 2002 kenan. Daga baya da ya fara waƙa.
“Kasancewar ni ma ina da sha’awar abin, kuma ina kallon yadda ya ke rubuta waƙa, sai ni ma na fara rubutawa. Idan na rubuta sai in kai masa in akwai gyara ya gyara min. Haka dai ya riƙa ba ni shawara ni ma in mai da hankali ga waƙa, amma a wancan lokacin Allah bai nufa ba.
“Bayan na dawo Kaduna, sai na buɗe shagon ɗinki na kai na. Daga nan sai na riƙa neman inda zan samu situdiyon buga waƙa. To daga nan dai na miƙe, na jaraba na ga kuma zan iya. Na rera waƙa ta ta farko mai taken ‘Kibiyar Ƙauna’.”
Ya Shaga zai kwatanta sana’ar waƙa da ta ɗinki a ɓangaren samun alheri? Sai ya ce, “Gaskiya na fi samun alheri a waƙa, saboda waƙa ta haɗa ni da mutane daban-daban domin ina waƙar fim, ina ta siyasa, sarauta, da kuma ta bukukuwa. Ka ga ban da arzikin kuɗi akwai na mutane kuma kenan.
“Na haɗu da manyan mutane da dama, waɗanda in ban da waƙar ba ni da hanyar da zan iya haɗuwa da su ballantana su san ni har in samu alheri daga gare su.”
Danganr da inda ya ke ganin mawaƙa su na buƙatar gyara, ya ce, “Akwai buƙatar mu kyautata ɗabi’un mu, domin kullum kalaman mu a cikin waƙoƙin kira ne ga shiriya, to don haka kai mai kira ga shiriya ya kamata ka tabbatar da cewa kai kan ka shiryayye ne, ba wai a fatar baki kawai ba.”
Game da dangantakar sa da Ala kuma cewa ya yi, “Aminu Ala maigida na ne. Kuma ya na zaunar da ni ya ba ni shawarwarin yadda zan gudanar da harkokin waƙa ta, da kuma zamantakewa da abokan sana’a ta. Ya ɗauke ni tamkar ƙanen sa wanda su ka fito ciki ɗaya.

“Don haka ni tsakani na da Ala sai dai godiya, don ba ni da abin da zan ba shi a kan riƙon da ya yi min, kuma ya sanya ni a hanyar samun abinci, kuma ina kan samun alheri da ita. Alhamdu lillahi.”
Mawaƙin ya yi godiya ga dukkan masoyan sa, ya kuma yi masu fatan alheri, da fatan Allah ya bar zumunci tsakanin sa da su. Ya kuma yi addu’ar Allah ya ƙara haɗa kan mawaƙa, ya kuma ɗaukaka sana’ar su da su kan su mawaƙan.