• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Harkar fim ta sauya mani rayuwa – jaruma Amina A. Shehu

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 26, 2022
in Taurari
0
Amina A. Shehu

Amina A. Shehu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AMINA A. Shehu sabuwar jaruma ce a Kannywood wadda ta sha alwashin samun nasara a burin da ta ke so ta cimmawa a game da shigowar ta wannan masana’anta nan ba da jimawa ba. A cewar ta, a yanzu har ta fara ganin hasken cikar burin nata.

Tun da farko, a tattaunawar ta da mujallar Fim, jarumar ta bayyana cewa ita haifaffiyar Zariya ce, inda a nan ta yi makarantar firamare, sai kuma ta yi sakandare a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. Daga nan ta dawo Kano domin ta shiga harkar fim.

Amina, wadda ‘yar shekara 23 ce, ta ce, “A lokacin da zan shiga fim sai na zo Kano. Da man akwai gidan ‘yan’uwa na a Kano, don haka sai na dawo gidan da zama. Da haka na samu na shiga harkar fim ɗin.”

Ta ƙara da cewa, “A shekarar 2018 na shiga harkar fim, kuma daga lokacin zuwa yanzu na yi finafinai da dama. Amma dai waɗanda zan iya tuna sunan su akwai ‘Gidan Danja’, ‘Gidan Mato’ ‘Wata Makauniya’, da sauran su.”

Amina A. Shehu

Da wakilin mu ya tambaye ta yadda ta samu kan ta a matsayin jarumar fim, sai ta amsa da cewa: “To, gaskiya na ji abin wani iri na daban, saboda ka san a lokacin da ban fara fim ba, ai rayuwar da na ke babu wanda ya san da ni, to amma kuma da aka fara gani na a fim sai rayuwa ta ta sauya. Don haka ni ina ganin harkar fim ta sauya mani rayuwa, don a baya duk abin da na so na kan iya yin sa cikin sauƙi ba tare da wani ya sani ba, amma a yanzu duk abin da zan yi, to sai na duba na ga me zai jawo a gare ni a wajen mutane, tunda a yanzu duniya ta fara ganin abin da na ke yi. Wannan ya sa harkar fim ta sauya mani rayuwa ta.”

Akwai wani ɓangaren ma inda harkar fim ta sauya wa Amina rayuwa, wanda kuma ya shafi burin da ta ke da shi a ran ta. Wannan ko shi ne harkar kasuwanci da ta ke yi. A cewar ta: “A gaskiya, ni da man ina harkar kasuwanci. To sai ya zama ba a san ni ba, don haka ko da na saro kayan ma sai na daɗe ban sayar ba. Amma a yanzu da na fara harkar fim, sai na ƙara samun ciniki. Kuma ni da man babban buri na shi ne na yi amfani da fim na yi suna don ya zama na yi amfani da damar a wajen kasuwancin da na ke yi.

“To a yanzu ka ga daga na saro kaya ya ke ƙarewa, saboda wasu sun san ni a fim, su na sayen kayan saboda sun san ni ‘yar fim ce, ina burge su, don haka ina ganin burin da na ke da shi na shigowa harkar fim na same shi.”

Amina ta yi kira ga masu harkar fim da su gane akwai hanyoyi da dama da za su yi amfani da harkar fim domin su tsaya da ƙafar su ba tare da sun yi fim ba. “Kawai dai su yi amfani da damar da su ke da ita ta sunan da su ka samu a harkar fim, domin su gina rayuwar ta gaba ko da bayan sun bar harkar fim ɗin sun yi aure,” inji ta.

Loading

Tags: Amina A. ShehuGusauharkar fimjarumaKannywoodKanokasuwancisauyin rayuwaZariya
Previous Post

Jarumar Kannywod, Madam Korede ta yi adabo da Nijeriya, ta na barar addu’a

Next Post

Ni tela ne, amma na fi samun arziki da waƙa – Shehu Shaga

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Shehu Shaga

Ni tela ne, amma na fi samun arziki da waƙa - Shehu Shaga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!