NIJERIYA da ƙasar Spain sun ƙudiri aniyar haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin sun haɓaka harkar fim a nan ƙasar.
Hakan ya biyo bayan ganawar da Manajan Daraktan Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, ya yi da Jakaden Spain a Nijeriya, Juan Ignacio Sell, a ofishin jakadancin Spain da ke Abuja a ranar Litinin.
A lokacin ganawar, Ali ya yaba wa jakaden kan cigaba da ba da tallafi ga NFC da Spain ke yi, musamman wajen bunƙasa masana’antar finafinai, inganta aiki da ayyukan bunƙasa ma’aikata, shirye-shirye da ayyuka.
Spain ta sabunta alƙawarin tallafawa da shiga cikin gagarumin Bikin Baje-kolin Fim na Zuma na shekarar 2024 wanda Nijeriya ke shiryawa; ƙaddamar da haɗin gwiwar makon bikin finafinai na Nijeriya da Spain; shirye-shiryen jagoranci da musanya don haziƙai masu tasowa ta hanyar Cibiyar Finafinai ta Ƙasa da ke Jos; tallafin fasaha da baiwa domin Ma’ajiyar Finafinai, Bidiyo da Sauti ta Ƙasa, wato National Film Video & Sound Archive (NFVSA) da ke Jos.
Batun ɗabbaƙa yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Spain dai shi ne ya mamaye tattaunawar a wurin ganawar.

Ziyarar wani ɓangare ne na sabon ƙudirin NFC na yin amfani da damar da za a bi wajen jiɓintar ƙasashen ƙetare don inganta gudunmawar masana’antar finafinai ta Nijeriya da bunƙasa yanayin ƙirƙire-ƙirƙire na cikin gida da na duniya.
A ziyarar, waɗanda su ka rufa wa Alhaji Ali baya su ne Mista Edmund Peters, Daraktan Shirye-Shirye da Bada Tallafi ga Industiri na hukumar ta NFC, da Mista Jeremiah Nyam, shugaban Sashen Bikin Baje-kolin Finafinai.
