FITACCIYAR jaruma Rahama Sadau ta buɗe wata katafariyar masana’anta mai ƙunshe da harkokin kasuwanci da ta mallaka, ciki har da sashen abincin sayarwa da na gyaran gashi.
Sunan wajen ‘Sadauz Home’ kuma ya na nan a gida mai lamba 27 Titin Raɓah, cikin garin Kaduna.
An buɗe wajen a jiya Talata, 10 ga Disamba, 2019 wanda ya zo daidai da ranar murnar zagayowar ranar haihuwar ta.
Wajen ya ƙunshi ɓangarori da dama, waɗanda su ka haɗa da wajen cin abinci (‘resturant’) da wurin aski na maza da wurin gyaran gashi na mata da wurin shan askirim (‘ice cream’) da na cin shawarma. Akwai kuma wurin shan shisha da na buga ƙwallon sunuka (‘snoocer’).
A sashen sayar da abincin, su na yin na gargajiya da na zamani, har da na ƙasar waje.
Haka kuma gidan ya ƙunshi wajen ɗaukar hoto na ‘Sadau Pictures’.

Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa ɗaya daga cikin ƙannen Rahama, wato Zainab Sadau, ita ce manajar kamfanin wadda za ta riƙa gudanar da shi, “saboda ita Rahama ba mai zama wuri ɗaya ba ce”.
A lokacin taron buɗe wurin, Rahama Sadau ta cashe da rawa, musamman lokacin da fitaccen mawaƙin nan mai suna Classiq ya ke nishaɗantar da taron.

Classiq shi ne mawaƙin da ya fito a bidiyon wata waƙa mai taken ‘Love’ tare da Rahama, bidiyon da ya janyo ƙungiyar MOPPAN ta kori Rahama daga harkar fim a shekarar 2016.
A bikin na buɗe ‘Sadauz Home’, jarumar na sanye da wata doguwar riga ja wadda aka tsaga gefen ta, sannan kan ta babu ɗankwali.
Ɓullar hotunan taron ya haifar da surutu a soshiyal midiya kan irin shigar da jarumar ta yi.
Shi dai wannan bikin, an yi shi ne cikin sirri, wato ba kowa da kowa aka gayyata ba, sai zaɓaɓɓun mutane makusantan Rahama.

Wasu daga cikin su sun haɗa da Umar UK, Fati Washa, Hadiza Gabon, Umar M. Shareef, Classiq, da ‘yan’uwan Rahama na jini da kuma ƙawayen ta da sauran abokan arziki.
Kowa na ta fatan Allah ya ɗaukaka ‘Sadauz Home’, ya kuma kawo kasuwa.
Wannan abu da Rahama Sadau ta yi ya bambanta da yadda sauran ‘yan’uwan ta mata ‘yan fim ke yi wajen kama sana’a ba dogaro da harkar fim kawai ba.

Duk kusan matan industiri dai su na buɗe shaguna, amma dai yawancin su kusan sana’a iri ɗaya su ke yi – ko dai sayar da tufafi da kayan kwalliya ko saida abinci ko gyaran gashi.