RANAR 1 ga Oktoba, 1960 aka ba wa ƙasa ta Nijeriya ‘yanci. Yau 1 ga Oktoba 2021. Shekara 61 kenan.
A lokacin da na ke rubutun nan, mun kwana uku kenan a jere ba wuta. Na taɓa yin hira da wani ɗan ƙasar Cana ɗan kimanin shekara 34 a duniya a birnin Guangzhou, ya ce min sai da ya girma sannan ya fahimci cewar wutar Nepa ba halitta ba ce ita ma, aikin kimiyya ce. Ya ce da ya ɗauka halitta ce kamar rana da wata da taurari.
Amma mu a ƙasar mu Nijeriya hatta a Abuja wutar Nepa ba ta tsaya da ƙafafun ta ba, tsawon shekaru 61.
Mu dawo fagen kiwon lafiya. A wannan rana irin ta yau, a ƙasa ta Nijeriya har yanzu likitoci yajin aiki su ke yi. Gwamnati ta kasa zaunawa ta sasanta da su.
Batun ilmi ya gurgunce. Kowane lokaci ana cikin yajin aiki.
Batun tsaro kuwa, wannan ya fi komai lalacewa. Kusan ko’ina a Arewa sai dai hamdala. Wasu mutanen idan abu bai shafi inda su ke kwanciya ba, su ba sa kawo abin a ran su a matsayin matsala.
Bala’in da mutanen Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja, Sakkwato da Kebbi su ke ciki na kidinafas da bandit ya fi na Boko Haram ɗin da aka yi fama da shi a yankin Maiduguri da Yobe.
Matsalar ruwan sha, ita ma har gobe ana fama da ita.
Matsalar Kayan abinci da tsadar rayuwa. Matsalar noma da kiwo. Matsalar fyaɗe da kashe-kashen aure.

Fatan mu da burin mu kawai yanzu shi ne Allah ya kawo mana shugabanni nagari, adalai, waɗanda za su gyara ƙasar mu Nijeriya.
Lokacin da na ke rayuwa a ƙasar Sin, wato Cana, garin su Zainab Zhang, na kan yi mamakin wai mutanen da ba su yarda da samuwar Allah s.w.t. ba su ne su ke wannan mulki na adalci a ƙasashen su. Su su ka gina ƙasashen su ta yadda in aka rufe wa ɗan Nijeriya ido ko aka yi masa allurar barci aka kai shi ƙasar idan ya farka aka ce masa ai mutuwa ya yi aka sa shi a Aljanna, zai yi amanna da hakan.
Mu kuwa a ƙasa ta, an yarda da Allah da ranar Lahira ɗin, amma adalci ya kasa wanzuwa a tsakanin mu. Har talakawan a nan adalci ya yi mana ƙaranci, ba ma iya yi wa kan mu.
Allah ka raba mu da nadama da ƙasƙanci da bauta a rayuwar mu ta duniya da lahira.
* Larabi Larabeen fitaccen marubuci ne kuma ɗan kasuwa a Kano