A YAU ne Nijeriya ta cika shekaru 61 da samun mulkin kai daga ƙasar Birtaniya. A yayin da ɗimbin ‘yan Nijeriya ke bikin murnar zagayowar wannan rana, su ma ‘yan fim ɗin Hausa ba a bar su a baya ba; sun yi hotuna iri daban-daban sanye da kalolin tutar Nijeriya (fari da tsanwa) don nuna tasu murnar.
Daga fitattu irin su Ali Nuhu zuwa ga waɗanda ba su yi fice ba, maza da mata, duk sun yi irin waɗannan hotunan tare da rubuta saƙonnin taya murna, wato irin “Happy Independence Day” da sauran su.
Daga ƙasar Indiya, Rahama Sadau, wadda ta je can domin ɗaukar wani fim na Bollywood kamar yadda mujallar Fim ta labarta maku, ta yi hotuna tare da Jakaden Nijeriya Ambasada Ahmed Sule.
Kai, hatta Maryam Yahaya, wadda ke zaune a gida ta na jinya, ta wallafa hotunan ta guda biyu inda ta taya sauran ‘yan Nijeriya murnar wannan rana. An gan ta a rame sosai, har ma wasu sun yi mata ƙarin addu’ar samun lafiya.
Ga kaɗan daga cikin hotunan, mujallar Fim ta kawo maku domin ku goge kwantsar ido:
Rahama Sadau tare da Jakaden Nijeriya a ƙasar Indiya, Ambasada Ahmed Sule, sun yi hoto a gaban fosta mai bayyana zagayowar cikar ƙasar mu shekara 61 da samun ‘yanci, a ofishin jakadancin Nijeriya na birnin New DelhiRahama Sadau sanye da tufafi mai kalar fari da tsanwa ta yi hoto don bayyana murna kan zagayowar cikar ƙasar mu shekara 61 da samun ‘yanci, a ofishin jakadancin Nijeriya na birnin New DelhiJarumar Kannywood, Aisha Ahmad Idris (Ayshatulhumaira) na murnar cikar Nijeriya shekara 61 da samun ‘yanciFitacciyar mawaƙiya Khairat Abdullahi (a dama) tare da ƙawar ta Halima sun yi shiga don nuna murnar cikar Nijeriya shekara 61 da samun ‘yanciDaga hagu: Aisha ‘Izzar So’, Lawan Ahmed, Momee Gombe da Garzali Miko sun yi shiga don nuna murnar cikar Nijeriya shekara 61 da samun ‘yanciFitacciyar jaruma Saima Mohammed Raga sanye fa farin mayafi a gaban tsanwan bango ta wallafa saƙon taya murna kan cikar Nijeriya shekara 61 da samun mulkin kaiDuk da rashin lafiyar da ta ke fama da shi, fitacciyar jaruma Maryam Yahaya ta sanya farar riga da koriyar hana-sallah tare da tura saƙon taya murna kan cikar Nijeriya shekara 61 da samun mulkin kaiBa a bar jaruma Hassana Muhammad a baya ba wajen yin shiga da tufafi mai ratsin kalolin tutar Nijeriya don bayyana murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun ‘yanciFitaccoyar jaruma kuma furodusa Mansurah Isah ta yi shigar kalolin tutar Nijeriya don murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun mulkin kai.Mawaƙin hip-hop Ɗanmusa New Prince sanye da babbar riga da aka yi da kalolin tutar Nijeriya Jaruma Jamila Usman (Lasco) sanye da riga mai kalolin tutar Nijeriya don murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun mulkin kai.Jaruma Jamila Usman (Lasco) sanye da riga mai kalolin tutar Nijeriya don murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun mulkin kai.Sarkin Waƙar Sarkin Dutse, Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa (a tsakiya), ya saka tufafi masu kalolin Nijeriya kuma ya tura saƙon taya murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun mulkin kaiFitaccen jarumi kuma furodusa Tijjani Asase tare da ɗan sa sun yi shigar musamman don murnar cikar Nijeriya shekaru 61 da samun mulkin kaiFitaccen mawaƙi Abubakar Sani (Ɗanhausa) ya yi hoto a gaban tutar Nijeriya tare da tura saƙon taya murnar cikar ƙasar nan shekaru 61 da samun mulkin kai