SANANNEN mawaƙin siyasa a Kannywood, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya ba da kwangilar gyaran hanyar Kwanar Darmanawa zuwa Gandun Sarki da ke birnin Kano.
Mai taimaka wa mawaƙin na musamman a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, shi ne ya ba da sanarwar ba da aikin hanyar.
Ya ce mawaƙin ya ba da aikin ne a yau Laraba, 11 ga Satumba, 2024, inda shi da tawagar sa suka ziyarci wurin aikin tare da ma’aikatan kamfanin da za su yi aikin.

Da yake jawabi a wurin, Rarara ya ce, “Na ba da umarnin fara aikin nan take, domin abubuwan da yake faruwa a kan hanyar ya yi yawa.”
Ya ƙara da cewa, “Daga yanzu babu sauran face-face a kan hanyar.”
Da yake jawabi a wurin, Mai Unguwar Darmanawa ya tabbatar wa da Rarara cewa masu ciki suna shan wuya wajen wucewa a kan hanyar, inda har wasu daga cikin su suna samun matsalar zubewar cikin saboda matsalar hanyar.

Haka kuma ya yi wa mawaƙin godiya bisa wannan babban aiki da ya ɗauki nauyin yi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Rarara ya yi irin wannan aiki ba. Idan ba ku manta ba a Satumba, shekarar 2023, mawaƙin ya ba da gyaran hanyar karkarar su, waɗanda suka haɗa da hanyar Tudun Wakili zuwa Sandu zuwa Ɗanja zuwa Dabai; hanyar Kahutu zuwa Ceɗiya, daga Ceɗiya kuma zuwa Zarewa.