SHAHARARREN mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya cika alƙawarin gasar da ya saka na waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, wadda ya rera wa ɗan takarar shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan ya lashe zaɓen fidda gwani a jam’iyyar APC.
Ya yi hakan ne a wani ƙwarya-ƙwaryan taro da ya shirya a Katsina a jiya Asabar.
Kamar yadda shugaban taron, Rarara, ya bayyana, an samu sama da mutum 3,000 da su ka shiga gasar.
A ranar Asabar, 11 ga Yuni, 2022 aka ba da sanarwar yadda za a shiga gasar, aka ce ‘yan TikTok za su yi bidiyo su na mamin waƙar, inda za su ɗora a shafukan su na TikTok ɗin.
Aka ce waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3 za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 zuwa na 10 kuma za a ba su kyautar wayar hannu ƙirar Iphone-13 Pro Max.
Su kuma ‘yan Instagram da Facebook, an buƙace su da su yi bidiyon waƙar wanda bai wuce ƙasa da cikakkun minti biyu ba, a gefe da gefe kuma za su saka hoton Tinubu da na APC.

Su ma waɗanda su ka lashe gasar, daga na 1 zuwa na 3, za su samu kyautar mota kowannen su, daga na 4 zuwa na 10 kuma kyautar waya ƙirar Iphone-13 Pro Max.
Haka kuwa aka yi, bayan ɗaukar kimanin wata biyu da wasu kwanaki ana tantance bidiyoyin da aka yi na shiga gasar, a jiya Asabar, 27 ga Agusta, 2022 aka shirya gagarumin bikin ba da kyaututtuka ga zakarun gasar.
An fara bikin da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ɗakin taro da ke Local Government Service Commission, Katsina.
Da farko an bayyana waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 3 a dukkan ɓangarorin biyu tare da miƙa masu kyautar motocin su.
Wanda ya zo na 1 an ba shi Honda (Discussion Continues) a ɓangaren bidiyo, haka shi ma na ɓangaren Tiktok ya samu Honda (Discussion Continues), inda sauran huɗun su ka samu Honda (EOD).
Haka zalika, daga na 4 zuwa na 10 a kowane ɓangare ya samu Iphone-13 Pro Max.
Sannan kuma an ƙara zaƙulo mutum 200 a cikin waɗanda su ka shiga gasar, an ba kowanne daga cikin su N100,000 a matsayin ihsani na shiga gasar.
Mutane daban-daban ne su ka shiga gasar, kuma mafi yawan su matasa ne maza da mata.

