• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa na yi rawa da ‘yan mata a dandali – Tahir Fagge

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 29, 2022
in Tattaunawa
2
Tahir Fagge na rawa da bin waƙar Hamisu Breaker tare da matashiyar mace a dandamalin gala

Tahir Fagge na rawa da bin waƙar Hamisu Breaker tare da matashiyar mace a dandamalin gala

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A KARON farko, fitaccen jarumin finafinai Hausa, Tahir Mohammed Fagge, ya ɓara kan dalilin da ya sa ya yi rawa tare da wasu matasan mata a bainar jama’a a wajen wasan gala.

Tun a farkon 2020 ne aka fara yaɗa bidiyon rawa da waƙar da Tahir ya yi tare da matan a wani wasan gala, inda aka gan su su na bin wata waƙar Hamisu Breaker Ɗorayi, to amma bidiyon bai haifar da surutai ba sai a bana lokacin da aka ƙara wallafa shi a soshiyal midiya, musamman a TikTok da YouTube.

Da yawa waɗanda su ka kalli bidiyon sun ce jarumin bai kyauta ba da aka gan shi ya na rawa da yaran mata sa’annin jikokin sa.

Sai dai a tattaunawar da ya yi mujallar Fim kwanan nan, Tahir Fagge ya kare kan sa tare da yin kakkausan martani ga masu cewa abin da ya yi bai kyauta ba.

Ya faɗa wa mujallar cewa ya na jin duk maganganun da ake yi a ciki da wajen industiri dangane da bodiyon. Daga nan ya ɗauko bayanin yadda abin ya faru tun daga tushe, kamar haka: “Lokacin da abin ya faru, ina kwance ne a gida, ba ni da lafiya; na samu matsalar cutar shanyewar ɓarin jiki, har ya zama ba zan iya tafiya mai tsayi ba a lokacin har sai na zauna na huta. Kuma ba ni da kuɗin da zan je asibiti, kuma ina neman kuɗi N260,000 wanda da shi ne za a ɗauki hoton zuciya ta, za a ɗauki hoton ƙirji na da yi mani magani.

“Yaran nan su ka zo har gida su ka same ni, su ka ce ko da ba zan yi rawa ba, su na so na je wajen na zauna a matsayi na na babban baƙo. Kuma a nan su ka ɗauki kuɗi N160,000 su ka ba ni. Ka ga saura N100,000 kenan.

Jarumin ya yi shame-shame kan dandamali a daidai wani baitin waƙar inda ake maganar macewa saboda soyayya

“A lokacin na ga duk wanda ya faɗa ruwa idan aka ba shi takobi zai kama, don ya na neman ceto. Da na je wajen na zauna sai masoya su ka roƙe ni da na tashi ko tsayawa na yi a kan fulo, su ka samo tsohuwar waƙar da na hau tun a finafinan baya su ka saka. Sai aka riƙa yi mani liƙi, wanda kuma alhamdu lillahi a wannan lokacin na samu cikon N100,000 ɗin da na ke nema da zan haɗa a yi mani aikin, har ma da wasu kuɗin da na riƙe a hannu ina ci da iyali na lokacin da na ke zuwa asibitin.

“Amma su da su ke maganar, me su ka yi mani don ceto rayuwa ta?

“Kuma ko a lokacin da na bar gari waye ya yi tunanin ko ‘ya’yan su na cin abinci ko su na zuwa makaranta, su na da lafiya, ya su ke rayuwa?

Babu wanda ya yi tunanin wannan a masana’antar ta Kannywood. Sai kawai mutum ya riƙa surutu a kan ka!

“Da fa mutum ya ba ka wata gudunmawa, shi ne zai yi surutu a kan ka. 

“Waɗanda su ka ba ni gudunmawar su lokacin da ba ni da lafiyar nan ba su wuce mutum huɗu ba. Rarara ya ba ni N20,000 da na ce masa zan sayi magani. Abdul Amart ya ba ni 15,000. Bashir Maishadda ya ba ni 20,000. Wannan su ne, a lokacin ina neman N260,000.

“Shi kenan, sai na zauna na kashe kai na ko na shiga wani yanayin da za mu rasa inda za mu saka kai ni da iyali na, ban tashi na nemi magani ba?

“Yau ka na barin masana’antar nan babu wanda zai yi tunanin bayan ka. Yanzu ka duba Tijjani Ibraheem, kaɗan ne su ke tunanin bayan sa.

“Yanzu akwai waɗanda su ke tunanin sun gayyace ni fim na ƙi zuwa. To su kawai lafiyar ka su ke nema, daga sun mori lafiyar ka shi kenan.

“Don haka wannan shi ne dalilin da ya sa na tashi tsaye domin samar wa kai na mafita. Kuma duk masu yin surutun su je su yi ta yi!”

Tare da wata jarumar a dandamalin gala
Wani ɗan kallo na yi wa Tahir Fagge liƙi
Tahir Fagge tare da su Maryam Yahaya

Loading

Tags: galaKannywoodmartanimatarawaTahir Fagge
Previous Post

Rarara ya yi wa zakarun gasar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ ruwan naira da motoci da waya

Next Post

Ayyiririi! Mawaƙiya Hajjo Idi Moris ta yi miji

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Hajara Idris Moris

Ayyiririi! Mawaƙiya Hajjo Idi Moris ta yi miji

Comments 2

  1. Pingback: Abin dayasa nake rawa da ‘yan mata a Gidan Gala – Tahir Fagge ya magantu » Labarai
  2. Pingback: Dalilin da ya sa na yi rawa da ‘yan mata a dandali – Tahir Fagge - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!