• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rashin tsoro ya sa na fito a ɗan Boko Haram, inji Mustapha Hamid, Zayyad na ‘Daɗin Kowa’

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 3, 2018
in Taurari
0
Mustapha Hamid

Mustapha Hamid

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUK wanda ya ke kallon wasan kwaikwayon nan mai farin jinni na ‘Daɗin Kowa’ ya san mutumin da ake kira Zayyad, wanda ya ƙware wajen shirya ta’addanci. To, Zayyad ba wani ba ne sai Mustapha Hamid wanda har ila yau ake kira da Mista Indiya. Matashin jarumi ne da ya kasance mara tsoro. Hakan ne ma ya ba shi damar rawa hawa rol ɗin Zayyad domin kuwa a lokacin da aka fara shirin na tashar talbijin ta Arewa 24 duk wani jarumi da aka ce za a ba shi rol ɗin sai ya ce ya na jin tsoro, amma shi ya karɓa ya riƙa fitowa a rol ɗin. Kuma wani abin mamaki sai rol ɗin ya dace da shi.

Domin jin ko wanene Mustapha Hamid da kuma yadda aka yi ya samu shiga ‘Daɗin Kowa’, wakilin mu a Kano, MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da shi.

FIM: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatun mu.

MUSTAPHA HAMID: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Mustapha Hamid, wanda aka fi sani da Mista Indiya. Kuma tarihin rayuwa ta ni ɗan asalin Jihar Bauchi ne. Na yi rayuwar karatu na na firamare da sakandire a garin Zariya. Sannan kuma na yi karatu na na gaba da sakandire a garin Kano wanda kuma a yanzu a nan na ke ci gaba da zama. Kuma an haife ni a ranar 12 ga watan Fabrairu, 1984. A halin yanzu ina da mata ɗaya da yaro ɗaya.

FIM: Da yawa mutane su na kiran ka da suna Mista Indiya. Yaya aka yi ka samu wannan suna?

MUSTAPHA HAMID: To, sunan Mista Indiya ya samu ne tun lokacin yarinta, da yake mahaifiya ta ta na da alaƙa da ƙasar Indiya. To, idan aka saka mana fim ɗin ‘Mister India’ mu na kallo, sai ya zamana agogon da yake hannun Mista India ya na burge ni, don haka duk lokacin da za ta je ƙasar Indiya wajen iyayen ta sai na ce idan ta je ni tsarabar da za ta kawo min irin wannan agogon na Mista India. To da haka dai na samu wannan suna, kuma har na taso da shi zuwa yanzu.

FIM: Ya aka yi ka shigo Kannywood?

MUSTAPHA HAMID: Na samu kai na ne a wannan masana’anta a 1999. Ko da yake tun a wancan shekarun na ke, amma har yanzu ba a san da zama na ba. To da man ita harka haka ta ke. Kuma a lokacin ina sakandire, lokacin da aka zo za a yi wani fim aka nemi waɗanda za su fito a cikin fim ɗin, kasancewar fim ɗin ya na ƙunshe ne da ɗaruruwan mutane, su kuma masu fim ɗin ba za su iya biyan kowa kuɗin sallama ba, sai ya zamana ana neman waɗanda  za su bada gudunmawa. Kuma ni sai na ji ina da ra’ayi, kawai sai na shiga na je aka yi fim ɗin da ni. Wannan fim ɗin kuma sunan sa ‘Shahidin Karbala’.

FIM: A tsawon lokacin da ka yi, ko za ka iya tuna yawan finafinan da ka yi?

MUSTAPHA HAMID: To, da yake lokacin da aka yi fim na farko ina rayuwar karatu ne, to ka ga ban ɗauki fim a matsayin sana’a ba, kuma a lokacin su daraktocin da yake ’yan Kannywood ne, sun yi sha’awar cewar su na da buƙatar na ci gaba da fim, amma sai ya zama karatu ne a gaba na. Don haka ba zai yiwu ba. Saboda haka na kan yi shekara ɗaya ko biyu  ban fito a fim ba, don haka ban da na farko finafinan da zan iya tunawa na  yi su ne ‘Arba’, ‘Shahid’, ‘Babbar Mace’, to da dai sauran waɗanda a yanzu ba zan ya tunawa da su ba.

FIM: Da yake harkar fim ɗin ta na da faɗi, ko ka yi wata harkar bayan aktin a cikin masana’antar?

E, bayan aktin na yi wasu abubuwa waɗanda ma ba a cikin industiri ɗin ba waɗanda su na da alaƙa da ita, domin na yi aikin jarida, inda na zama wakili kuma marubuci a wata jarida kuma a cikin industiri. Kamar maigida na Adam M. Adam, lokacin da na zo Kano mu ka haɗu da shi sai kawai ya ce shi abin da ya ke buƙata na zama mai aiki a bayan kyamara duk da cewar a lokacin ba ni da ra’ayin hakan, amma duk lokacin da aka ba shi aikin fim a matsayin darakta sai ya ba ni mataimakin sa.

FIM: To an san ka a shirin ‘Daɗin Kowa’ da ka ke fitowa a matsayin Zayyad. Ko yaya ka yi ka samu kan ka a cikin shirin?

MUSTAPHA HAMID: Shi ‘Daɗin Kowa’ tambayar za ta iya kasancewa a matsayi na na darakta, ko a matsayi na na ɗan wasa? Idan a matsayin darakta ne, na iya cewa su tashar Arewa sun ɗauke ni a matsayin Mataimakin Darakta a shirin ‘Daɗin Kowa’. Ko da yake lokacin da na je aiki an riga an fara shirin ‘Daɗin Kowa’, an yi episodes har guda biyar, don haka mun samu za a ci gaba ne ni da wani Abdulmajid Sunusi, wanda aka fi sani da Kunle John. To, na yi ta zama a matsayin Mataimakin Darakta har zuwa lokacin da aka yi episodes talatin, inda kuma daga nan aka fara ba ni matsayin darakta har zuwa na 101. Sai kuma aka sauya min wajen aiki.

To shi kuma abin da ya shafi aktin, shi wani lokaci ne da aka yi casting ɗin likita, lokacin da mu ka je za mu yi shutin shi da man a cikin asibitin sa ne mu ke yin sinasinan asibiti, sai mu ka ce shi ne zai fito mana a matsayin likita. Har ya amince, amma da mu ka je da yake gidan sa ya na haɗe da asibitin, da mu ka sanar da shi lokaci ya yi ya zo za mu fara, sai kawai matar sa ta fashe da kuka, wai ita ba ta yarda mijin ta ya fita a cikin fim ba! To, shi kuma ganin haka sai ya janye. Wannan ya sa mu ka zamo ba mu da wani zaɓi na wanene zai fito a likita.

To, da yake fita ɗaya ne, sai na ce ni kawai zan fito. Duk da yake wanda ya ke matsayin Mataimakin Daraktan a lokacin, Salisu T. Balarabe, ya ɗan nuna rashin yardar sa, amma daga baya da ya zama babu yadda za a yi sai na hau rol ɗin. Amma shi ma na yi ne ba da niyyar zan ci gaba da fitowa ba.

To, ana tafiya, da aka fara zuwa rikici a fim ɗin, an fara taɓo batutuwan Boko Haram, sai ya zamana su jaruman da ake so su hau rol ɗin Boko Haram, sai ya zamana su na jin tsoro; kowa idan aka ce ya hau sai ya ƙi yarda. To, sai aka rasa yaya za a yi. To kawai sai na ce a ba ni rol ɗin, babu wanda na ke jin tsoro. Don haka na ce tunda na taɓa fitowa a matsayin likita, su gina min labarin a kan sa. Don haka sai su ka tsara ni likita ne, ina da ilimi na na aikin likita da kuma na kimiyya, amma na fake da aikin asibiti ne ina aikata ta’addanci. Sai ya zama a cikin shirin ne ma na ke haɗuwa da ’yan Boko Haram yadda za su kai hari. To da haka dai na zama Zayyad a ‘Daɗin Kowa’.

FIM: Yadda ka ke fitowa a matsayin Zayyad a ‘Daɗin Kowa’, ya za ka kwatanta kan ka da yadda ka ke Mustapha ko Mista Indiya a waje?

MUSTAPHA HAMID: To, Zayyad a ‘Daɗin Kowa’ ya zo ya danne sunan Mista Indiya a waje. Saboda yanzu duk inda na haɗu da mutane kawai Zayyad su ke kallo, ba Mista Indiya ba. Don haka  yanzu kawai mutane su na kallo na a Zayyad ne.

FIM: Bayan fitowar ka a ‘Daɗin Kowa’ yaya mu’amalar ka da mutane ta ke kasancewa?

MUSTAPHA HAMID: To, dole ka san su masu kallo a ko yaushe su na sha’awar jarumi, musamman ma idan jarumin ya na fitowa a rol mai haɗari. Don haka babu wani abu da na ke fuskanta a wajen mutane sai ƙauna. Saboda a iya tsawon shekarun da na yi a cikin harkar fim har zuwa 2014 da na fara fitowa a ‘Daɗin Kowa’, ban fito a wani fim da ya sa na samu karɓuwa, mutane su ka san ni, kamar shirin ‘Daɗin Kowa’ ba. Duk da cewa na ɗauka mutane za su tsane ni saboda rol ɗin, amma sai na ga su na nuna min ƙauna. Kuma ni ban taɓa sa wa kai na burin na kambama kai na ko na wuce gona da iri a rol ɗin don na ja hankalin mutane ba. Kawai dai ina yin rol ɗin ne yadda ya ke; don a sauran finafinai na kan yi hakan don a  san ni, amma na ‘Daɗin Kowa’ ba na yin haka. Amma sai ya zama na fi samun karɓuwa.

FIM: Yanayin rol ɗin da ka ke takawa bai sa ko da a wani lokaci idan ka na yawo wasu idan su ka haɗu da kai su tsorata ba?

MUSTAPHA HAMID:  To, ba dai a guduwa, sai dai na kan zama abin tsokana, kamar lokacin da aka sauya min ɓangaren aiki. Idan na fita zan yi aikin haɗa rahoto sai ka ji yara sun zo sun taru su na cewa, “Ga ɗan Boko Haram ɗin nan na ‘Daɗin Kowa’!” Sai ya zama na zama abin tsokana a wajen yara. Amma dai ni wannan ba ya wani damu na saboda yanzu kan mutane ya waye; don ka fito a wani rol ba ya na nufin kai ɗin ne ba.

FIM: Ya ka ke ganin yadda harkar fim ta ke isar da saƙo?

MUSTAPHA HAMID: To, ita da man harkar fim manufar kafa ta kenan tun asali. Kuma ka ga shirin ‘Daɗin Kowa’ an yi shi ne don samar da hanyar da mutane za su kauce wa ayyukan ta’addanci da kuma yadda za su taimaki kan su wajen tallafa wa jami’an tsaro da bayanai da kuma abubuwa daban na taimakekeniya a rayuwar jama’a. Kuma ka ga saƙon ya na isa ga jama’ar da ake yi domin su.

FIM: A ƙarshe, wane saƙo ka ke da shi?

MUSTAPHA HAMID: Saƙo na na ƙarshe, mutane su ƙara wayewa da abubuwan da su ke zuwa sababbi, domin akwai masu amfani a cikin su da kuma marasa amfani, musamman ga matasa. Don haka sai su rinƙa lura da duk abin da za a zo musu da shi, su sa ilimi da basira wajen yin mu’amala da shi. Kuma daga ƙarshe ina yi wa masoya masu kallon mu fatan alheri. Na gode da irin ƙaunar da  su ke nuna mana.

Loading

Previous Post

Juyin zamani: Tsakanin gaɗa, Asauwara, Mamman Shata da ‘yan fiyano

Next Post

Abin da ya sa na guji harkar fim na koma aikin gona – Rabi’u Alrahuz

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Rabi'u Alrahuz

Abin da ya sa na guji harkar fim na koma aikin gona – Rabi’u Alrahuz

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!