MADUGU Uban Tafiya a Kannywood. Ibrahim Muhammad Mandawari shi ne jarumi na farko a Kannywood. Shi ne ake yi wa laƙani da Baban Soyayya ko ka ce Hausa Rajesh Khanna. Su ne su ka fara home video, kowa daga gare su ya kwaikwaya.
Mandawari, wanda ya yi rayuwar sa a film industiri, ya bada gudunmawar da tarihin Kannywood bai zai cika ba sai da shi, shi ne mutumin da ya kawo cigaba daban-daban a Kannywood.
Allah Ya ji da ran Mai Unguwar Mandawari.
* Auwal Muhammad Sabo babban furodusa ne kuma shugaban kamfanin Sarauniya Films, Kano