JARUMA kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya), ta ƙaddamar da wani katafaren waje na gyaran jikin mata mai suna ‘DY Utrat 85’.
An yi taron a yammacin ranar Laraba, 26 ga Oktoba, 2020 a Titin Guda Abdullahi da ke unguwar Farm Centre a Kano.
Tun da farko da ya ke jawabi a matsayin babban baƙo a taron, Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), ya ja hankalin mata da su riƙa gudanar da duk wata harkar kasuwanci da za su yi wajen kare mutunci da kuma darajar ta mata.

Ya ce: “Yanzu idan mu ka duba, wannan waje an tsara shi ne bisa kiyaye mutuncin duk wata mace da za ta zo wajen domin a yi mata gyaran jiki. Saboda yanayin tsarin wajen, mutum ko shi ya kawo matar sa, to sai dai ya ajiye ta ya tafi, don ba a yi wajen don mata ba. Ko da yake akwai wani ɓangare na gyaran jikin maza, amma dai ba a haɗe su ke ba.
“Don haka samar da irin wannan waje shi ne zai tabbatar da kiyaye mutuncin mu da na iyalan mu.”
Shi kuma jarumi Nura Hussain, cewa ya yi samar da wajen gyaran jiki da mata su ke yi a matsayin sana’a a yanzu wani cigaba ne da aka samu na inganta lafiyar jikin mata da kuma kyautata alaƙa a tsakanin su da mazan su.
A nata jawabin, Hajiya Ruƙayya Dawayya ta bayyana wajen a matsayin wani sabon salo na kasuwanci da ta fito da shi wanda babu irin sa.
“Wannan waje tunani na ne ya kawo na samar da shi saboda sha’awar da na ke da ita ta gyaran jiki da kuma kwalliyar mata har ma da maza,” inji ta.
“Don haka a wannan waje mun samar da kwalliya da gyaran jiki kala-kala irin na hasashe da dama, saboda amfanin mutanen mu.

“Kuma ba mu tsaya ga kwalliya ba, har kayan amfanin yau da kullum mu na sayarwa, kamar turaruka na wuta, mayuka. Sannan za mu iya zuwa har gida a yi wa mace kwalliya da gyaran jiki, ba sai ta zo nan ba.
“Don haka wannan tsarin namu ya bambanta da sauran wajen gyaran jiki, don mu namu na daban ne.”
Taron ya samu halartar ɗimbin ‘yan fim, irin su Saratu Giɗaɗo, Asma’u Sani, Hannatu Bashir Safna Aliyu Maru, da Fauziyya Maikyau.

