• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

by NAZIR ADAM SALIH
February 7, 2025
in Tsokaci
0
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

Nazir Adam Salih

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Nazir Adam Salih

1. Jemagu:

Wannan rukunin mafi yawa ‘yan boko ne, da kuma masu ƙaryar boko waɗanda ba wai fim ɗin Hausa ba, su duk wani abu da ya shafi Bahaushe ba sa ƙaunar sa.

Irin waɗannan rukuni sun fi ƙaunar finafinan Turawa, kai sun fi fifita fim ɗin mutanen Kudancin Nijeriya fiye da na Hausa. Su fim duk ma’anar sa da kyawun sa in dai na Hausa ne za su caccake shi ko da kuwa ba su tsaya sun ga abin da ke cikin sa ba.

2. Tattabaru:

Waɗannan rukunin ‘yan gargajiya ne, ‘yan alƙawari, su duk wani abu da ya shafi Hausa suna ƙaunar sa. Don haka duk irin fim ɗin da aka yi da Hausa, duk rashin kyawun sa da rashin ma’anar sa su suna jin daɗin kayan su.

Da yawa daga cikin su, suna da ƙarancin ilimin zamani da kuma wayewa ta zamani. Don haka ko da fim ya zo da shirme ko shashanci, kai ka jiyo, domin kai kake gane shirmen da shashancin, su kallon abin su za su yi, kuma babu abin da ya shafe su, domin abin da ke cikin fim ɗin ya yi daidai da saitin ƙwaƙwalwar su.

Irin su ne za ka yi fim, kana ganin ya yi ma’ana sosai a mahangar ka, amma su sai su ce bai musu kyau ba. Kai kuma in ba ka fahimce su ba sai ka yi ta faɗa kana cewa ga fim mai ma’ana sun ƙi kallo. To ai bai yi daidai da ƙwaƙwalwar su ba ne Malam.

3. Dakilai:

Wannan rukunin suna kamanceceniya da rukunin dakilan mutane (marasa sha’awa). Domin su ba su ma san menene daɗin fim ba. Da wanda ya yi kyau da wanda bai yi kyau ba, da wanda ya yi ma’ana, da wanda aka tafka shiririta su duk ɗaya ne a wajen su.

Ana iya samun rukunin waɗannan ‘yan kallo a cikin jahilai da masu ilimi, ‘yan ƙauye da ‘yan birni, wayayyu da kidahumai, ko’ina akwai irin waɗannan mutane.

Haka nan irin waɗannan mutane za ka ga idan ana kallon fim ana ta ihu ana jin daɗin sa ko kuma ana ta tsaki fim ya ɓata wa mutane rai, za ka ga su babu wani sauyi a fuskar su, domin a wajen su duk ɗaya wai makaho ya yi dare.

4. Gwanaye:

Waɗannan ƙwararrun ‘yan kallo ne, waɗanda ke ɗauke da rariyar tata a cikin kwanyar su. Irin waɗannan rukunin ‘yan kallo na iya kallon fim ɗin Hausa, ko na yammacin duniya, ko na gabashin duniya, kai ko wanne irin fim ma suna iya kallo, amma suna da zaɓi, ba komai suke kallo ba.

Su, in dai fim ya yi ma’ana ya yi kyau to ko daga ina yake za su kalle shi kuma za su yaba masa. Mafi yawan su sun fi daga cikin masu ilimin zamani, amma a kan sami tsirari daga masu ƙarancin ilimin zamani, amma waɗanda ke da buɗewar idanu ta yawon duniya.

Wannan tunani na ne, idan kana da naka, to mu haɗu a comment section. Na san kai ma ko ke ma ba za ki rasa wani ƙarin rukunin ‘yan kallon na fim ɗin Hausa ba.

* Nazir fitaccen marubuci ne mazaunin Birnin Kano

Loading

Tags: finafinan hausamasu kalloNazir Adam Salih
Previous Post

Masarauta a Sokoto ta tuɓe mawaƙi Sojaboy daga sarauta saboda aikata ‘baɗala’

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ba kamfanin Lenscope Media kwangilar naira miliyan 250 domin gina Gidan Shirya Finafinai na Jos da badalar Kano

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Tsokaci

Shekaru goma bayan sace ‘yan matan Chibok: Nijeriya ba za ta ƙara biyan kuɗin fansa ba

April 15, 2024
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ba kamfanin Lenscope Media kwangilar naira miliyan 250 domin gina Gidan Shirya Finafinai na Jos da badalar Kano

Gwamnatin Tarayya ta ba kamfanin Lenscope Media kwangilar naira miliyan 250 domin gina Gidan Shirya Finafinai na Jos da badalar Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!