LIKITAR cikin shirin diramar ‘Daɗin Kowa’ ta tashar talbijin ta Arewa 24, Fatima Isah, ta bayyana cewa saboda matuƙar son da ta yi wa harkar fim tun ta na ƙaramar yarinya, har mafarkin fim ta riƙa yi.
A tattaunawar da mujallar Fim, jarumar ta ce: “Tun ina ƙarama na ke sha’awar shiga harkar fim, don haka na shiga ƙungiyoyi na wasan kwaikwayo a makarantun da na yi. Kuma a yanzu alhamdu lillahi, na samu sa’ar shiga na zama cikakkiyar jaruma.
“Amma kafin na fara saboda son da na ke yi wa fim idan na kwanta har mafarkin fim ɗin na ke yi. Wannan ya sa idan mu na magana da mama na ina faɗa mata son da na ke yi wa fim, sai ta ce na yi addu’a, ‘idan akwai alheri a ciki Allah ya sa ki yi a sa’a’.

“To alhamdu lillahi, a yanzu ga shi na zama cikakkiyar jaruma a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ wadda duk duniya ana kallo na. Kuma duk inda na je ana kallo na a matsayin jaruma mai muhimmanci, saboda rol ɗin da na hau ya ƙara mani ƙima a wajen mutane.”
Duk mai kallon ‘Daɗin Kowa’ ba zai manta da likita ba saboda irin tausayin da ta ke nuna wa duk wani mara lafiya da ya je asibiti ya na buƙatar taimako.
Fatima ta ce saboda wannan rol ɗin da ta ke takawa, wasu ma sun ɗauka ita likita ce a zahiri.
Ta ce, “Wani abin mamaki, sai mutane a unguwar da na ke su ke ɗaukar ni likita ce ta gaske, har su ke zuwa don na duba su! Har ma akwai wani lokaci da wata ta zo haihuwa sai kawai aka kwaso ta aka kawo ta gida na, sai da na yi masu bayani ai ni ba likita ba ce.
“Don haka ya kamata mutane su gane fim daban, rayuwar mutum ta zahiri daban.”
Jarumar ta yi kira ga abokan sana’ar ta da su riƙe sana’ar tasu da mutunci. Ta ce, “Ita harkar fim sana’a ce, don haka bai kamata mutane da su ke harkar su riƙa mayar da kan su ‘yan iska ba.”
Comments 1