TSOHON jarumi a Kannywood, Hamza Adamu Indabawa, ya yi kira ga masu sha’awar shigowa harkar fim da su daina gaggawar sai sun cimma burin su cikin ƙaramin lokaci.
Jarumin ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawar da ya yi da mujallar Fim a game da harkar fim ta wannan lokacin.
Indabawa ya ce: “Ita harkar fim mataki-mataki ne, don haka ba wai daga mutum ya zo lokaci guda ake samun ɗaukaka ba. Ko da yake ana samu, amma ba kowane jarumi ya ke samun hakan ba, sai dai idan aka bi a hankali sai ka ga an kai ga matakin da ake so har ma a wuce hakan.”
Ya ci gaba da cewa, “Yanzu ka ga ni a masana’antar nan na shafe shekaru kusan talatin amma ba kowa ya san ni ba sai a wannan lokacin da aka sa ni a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’. Amma idan mu ka duba shekarun da mu ka yi, mun yi haƙuri ne kuma mu ka ga abubuwan rayuwa da su ka zama darasi a gare mu a cikin harkar wadda ta sa mu ka riƙe ta sosai, kuma mu ka riƙe mutuncin mu.
“A baya tun ina fitowa a matsayin saurayi, na wuce matakin, sai ya zama ban kai a saka ni a matsayin uba ba, sai dai a saka ni a matsayin ƙanen uba, har na zo lokacin da za a saka ni a matsayin uba. To don haka sai ya zama kusan duk jaruman nan mata, tun daga kan su Zainab Raga, Sadiya Gyale da sauran waɗanda su ka yi zamani da su duk na fito a matsayin uba a gare su. Kuma har zuwa yanzu Ina fitowa ne a matsayin uba. Kuma sai yanzu ɗaukakar ta zo.
“Don haka ina godiya ga Allah da ya kawo ni lokaci na. Kuma duk haƙuri ne ya sa na kai ga hakan bisa taimakon Allah.”
Jarumin ya yi kira ga matasa masu shigowa harkar fim da su rage gaggawa kuma su yi haƙuri, su kare mutuncin su, “domin hakan ne zai sa su kai ga cimma nasara.”
![]()







