“DUKKAN rai za ta ɗanɗana mutuwa”. Wannan wata aya ce da duk wani mai rai ya tabbatar da aukuwar ta, amma abin da yake a ɓoye a gare mu shi ne lokaci da wurin da Allah zai ɗauki ran namu. Yadda mu ka gudanar da rayuwar mu a zaman da mu ka yi a gidan duniya ya na da matuƙar tasiri da yadda al’umma za su karɓi labarin rasuwar tamu.
Mutum za iya fahimtar haka ne in ya lura da yadda al’umma su ka girgiza tare da shiga alhini a lokacin da aka sanar da rasuwar Sarkin Musawa, Alhaji Muhammadu Giɗaɗo Usman Liman, a ranar 2 ga Satumba, 2020. Ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Abin da ya fara faɗo mani a rai shi ne irin yadda ya gudanar da rayuwar sa, da yadda ya yi matuƙar tasiri a rayuwar al’ummar sa a matsayin sa na jagoran al’umma da kuma yadda ya shimfiɗa adalci a zaman sa na Sarkin Musawa daga cikin zuriyar Sarkin Katsina Muhammadu Dikkko. Ya yi tsayin daka na ganin ya riƙe kowa a matsayin uwa ɗaya uba ɗaya. Ya kuma riƙe zumunci ta hanyar zama jagora ga zuriyar gidan da ke mulkin masauratar Musawa da kuma tsatson Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, wanda shi ne ya fara sarautar Katsina daga zuriyar Sulluɓawa. Marigayin kuma jika ne ga Sarkin Kano, marigayi Abdullahi Bayero.
Tabbas, ya bar tarihi na yadda ya haɗa kan zuriya da al’ummar yankin Musawa a duk inda su ke a faɗin tarayyar ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya. Haka kuma marigayin shi ne kuma babban yaya ga shahararren malamin tarihin nan na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, marigayi Dakta Yusufu Bala Usman. Ya kuma rasu ya bar ƙannen sa huɗu, waɗanda su ka haɗa da Hon. Ahmadu Usman Liman, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Musawa/Matazu; da Hajiya Halima Abdulkarim Usman, da Alhaji Ado Usman Liman na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina, da kuma Hajiya Bilkisu Garba Usman.
Tabbas, rasuwar marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Giɗaɗo Usman Liman za ta haifar da babban giɓi, amma in mu ka kuma yi tafakkuri da cewa marigayin ya yi tsayin daka wajen tarbiyyantar da al’ummar da su ke tare da shi kuma bai ɓoye dukkan sirrorin ilimi da matakan mulki da ya gada daga kaka da kakanni ba, wanda hakan ya sanya kowa ka gani a cikin zuriyar gidan sa za ka samu mutum ne da ya san abin da ya ke yi, a kan haka sai mu miƙa godiya ga Allah a kan cewa lallai marigayi ya bar baya mai albarka.
An dai haifi marigayi Muhammadu Giɗaɗo ne a ranar Lahadi, 20 ga Yuni, 1943 (ya na da shekara 77 kenan Allah ya yi masa rasuwa). Ya yi karatun allo a hannun malamin sa marigayi Malam Iro Mai Mazuru a cikin garin Musawa, a shekarar 1950 zuwa 1954. Daga nan ya halarci Makarantar Elementare da ke Kankiya a shekarar 1955. Daga nan ne kuma aka zarce da shi Makarantar Firamare da ke garin Minna ta Jihar Neja a shekarar 1956 zuwa 1957. Bayan ya kammala karatun firamare ne ya wuce Makarantar Sakadire da ke garin Suleja ta Jihar Neja a shekarar 1958. Lokacin da aka ɗaga darajar makarantar zuwa Babbar Makarantar Sakadire sai ya ci gaba da karatun sa a nan Sulejan a shekarar 1963.
Bayan ya kammala karatun ne sai kuma ya wuce makarantar horas da malamai ta Bauchi. Wannan kuma bayan ya samu gagarumin nasarar lashe jarabawar da ya yi ne na shiga makarantar, inda ya fito da takardar shaidar malanta mai daraja ta biyu (Grade II). Ya kuma halarci karatuttukan ƙara ilimi a ciki da wajen ƙasar nan a lokuta daban-daban.
Ayyukan da marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Giɗaɗo ya yi a lokacin rayuwar sa sun haɗa da wakili a Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Jihar Kaduna daga 1974 zuwa 1978, sannan ya zama Babban Darakta Hukumar Adana Kayan Tarihi bayan da aka ƙirƙiro Jihar Kastina a 1994, sannan ya yi shugaban Hukumar Kula da Tsabtace Muhalli ta Jihar Katsina a shekarar 2005.
Alhaji Muhammadu Giɗaɗo ya karɓi lambobin girmamawa da kuma shaidar yabo da dama. Tabbas kuma marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Giɗaɗo mutum ne mai haƙuri da son cigaban talakawa. Ya na kishin ganin ƙasar Musawa ta ci gaba a kan haka. Ya kan tsaya ya ga ya taimaki talakawan sa, musamman a kan abin da ya shafi kare haƙƙin al’umma.
Haka kuma tarihi ya nuna cewa marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Giɗaɗo shi ne shugaban masarautar Ƙaramar Hukumar Musawa tun daga shekara ta 1965 har zuwa lokacin rasuwar sa. Ya yi wakilci a hukumar mulkin Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma daga 1970 zuwa 1974, da Ƙaramar Hukumar Kankiya daga 1974 zuwa 1975.
Ya yi wakili a Hukumar Kula da Ilimin Jihar Arewa ta Tsakiya daga 1970 zuwa 1974.
Bayan an naɗa shi Sarkin Musawa, Alhaji Muhamadu Giɗaɗo ya yi ƙoƙarin ganin cewa an bunƙasa harkar noma sosai ta hanyar tabbatar da samun takin zamani da sauran abubuwa da za su bunƙasa harkokin noma da abinci a yankin Musawa.
A ɓangaren lafiya, a zamanin sa ne aka gina asibitin garin Musawa da wuraren shan magani a dukkan garuruwan magaddai da wasu ƙauyukan da ke ƙasar Musawa. Sannan a zamanin sa ne aka haɗa garin Musawa da wutar lantarki sannan kuma aka gina mata babban dam. Kuma an samar da hanyar da ta taso daga Charanchi da zuwa Kafinsoli zuwa Matazu zuwa Musawa da ta ɓulle zuwa Kurkujen. Wannan hanya ta ƙara bunƙasa tattalin arzikin alu’mmar ƙasar Musawa.
Tabbas, an samu ƙaruwar arziki a fannonin rayuwar al’umma da dama.
Ganin irin yadda marigayin ya yi aiki tuƙuru na bunƙasa Jihar Katsina da ma yankin arewacin ƙasar nan gaba ɗaya, ya kamata gwamnatin Jihar Katsina a ƙarƙashin Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ta samar da wani dandamali da za a ci gaba da tunawa da ayyukan alherin da ya gudanar a lokacin rayuwar sa. Ta haka matasa masu tasowa za su amfana da darussan da ke tattare da rayuwar marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Giɗaɗo.
An dai yi jana’izar sa ne da misalin ƙarfe 5 na yamma a gidan sa da ke unguwar Sabon Gari a garin Musawa ta Ƙaramar Hukumar Musawa.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu mata, Hajiya Binta Lawal Aliyu da Hajiya Maijidda Nasiru Maska, da kuma jikoki 10.
Mu na addu’ar Allah ya albarkaci dukkan abin da ya bari, ya kuma ba mu haƙurin jure rashin. Mu na kuma addu’a tare da fatan Allah ya gafarta masa, ya kuma sa Aljanna ce makomar sa.