• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 12, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

by ABUBAKAR IBRAHIM
July 10, 2025
in Nijeriya
0
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Alhaji Mohammed Idris tare da shugabannin Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) da wasu jami'an ma'aikatar a lokacin ziyarar.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun cigaba sannu a hankali, inda ya danganta hakan da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar baƙuncin membobi da sababbin shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) da suka kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa.

Yayin da ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubale, Ministan ya ce gwamnati na samun cigaba a hankali kuma tana samun nasarar rage tsananin matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci.

“Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin arziki ba tukuna. Gaskiya ne! Ni ma na yarda. Amma ba za mu ce babu cigaba ko kaɗan ba.”

Ya ƙara da cewa: “Ko hukumomin ƙididdiga na duniya suna fara ba Nijeriya kyakkyawan matsayi. Muna ganin alamu na ɗagawa a hanyar da ake tafiyar da tattalin arzikin mu.”

Idris ya ce manyan matakan sauyi kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi suna fara nuna tasiri mai kyau a ƙasar nan.

Haka kuma ya bayyana cewa sama da ɗalibai 300,000 ne suke cin gajiyar shirin bayar da rancen karatu na gwamnati, wanda ke ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da kuma ciyar da su.

Ya ce: “Saboda wannan manufa da aka tsara ta gwamnati, sama da ɗalibai 300,000 na Nijeriya da a da ba za su iya zuwa makaranta ba ko kuma da suka riga suka bar makaranta, yanzu suna da damar komawa makaranta domin gwamnati tana biya masu kuɗin makaranta da na ciyarwa. Ba a taɓa samun irin wannan ba.”

A kan batun tsaro, Ministan ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai masu ƙarfi don shawo kan matsalolin tsaro, inda ya ce dakarun soji na samun nasarori a yaƙi da masu laifi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya roƙi kafafen yaɗa labarai da su goyi bayan ƙoƙarin da rundunonin tsaro suke yi, tare da guje wa bai wa masu laifi muhimmanci fiye da kima.

“Ina ta faɗa tun da farko cewa ba daidai ba ne mu a matsayin mu na ‘yan jarida mu riƙa ba waɗannan masu laifi, masu tayar da ƙayar baya, ‘yan ta’adda ko ɓarayi ko duk yadda za a kira su, fifiko fiye da ‘yan Nijeriya nagari,” inji shi.

Ya ce ya kamata kafafen watsa labarai su riƙa bayyana nasarorin da sojoji suke samu da sadaukarwar su, maimakon maida hankali kawai a kan hare-hare da rashin nasara.

Idris ya bayyana cewa ko da yake aikin kafafen watsa labarai ne su riƙa sa ido kan gwamnati ta hanyar suka mai amfani, wajibi ne su kuma riƙa bayyana nasarori da cigaban da ake samu.

A martanin sa kan Rahoton Gyaran Dokoki da ƙungiyar ta gabatar, Ministan ya ce zai tattauna da Ministan Shari’a kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, tare da kafa kwamitin musamman a ma’aikatar sa domin nazarin rahoton.

Ya jaddada cewa manufar gwamnatin Tinubu tana daga cikin ginshiƙan dimokiraɗiyya ita ce kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yancin kafafen yaɗa labarai.

Sai dai ya ja hankalin ‘yan jarida da su riƙa amfani da wannan ‘yanci cikin kishi da kishin ƙasa, tare da riƙon gaskiya da haɗin kai don ci gaban ƙasa.

Idris ya taya sababbin shugabannin ƙungiyar murna, tare da bayyana shirin sa na ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da kafafen watsa labarai.

Tun da farko a jawabin sa, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya, Dakta Sebastian Abu, ya bayyana cewa tawagar ta kai ziyara ofishin Ministan ne don gabatar da rahoton Kwamitin Sauya Dokokin Ƙungiyar a hukumance.

Ya bayyana cewa rahoton ya nuna wasu tsofaffin dokoki a kundin tsarin mulki da suka zama ƙalubale ga ‘yancin aikin jarida a Nijeriya, waɗanda ya dace a duba ko a cire su.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Alhaji Mohammed Idris yana karɓar rahoton Kwamitin Gyaran Mulki na Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya daga Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Dakta Sebastian Abu a lokacin ziyarar.

Loading

Previous Post

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

Next Post

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

Related Posts

Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Next Post

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!