A YAU Alhamis, 12 ga Afrilu, 2023 ne lauyoyin mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) su ka bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Zaki a Kano domin gabatar da kan su a matsayin masu tsaya masa a ƙarar sa da wani ɗan kasuwa ya shigar.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda ɗan kasuwar, mai suna Muhammad Ma’aji, ya maka Rarara a kotun a kan kuɗi naira miliyan goma da dubu ɗari uku (N10.3m) da ya ce ya na bin sa.
Mujallar Fim ta ƙara samun bayanin cewa ɗan kasuwar ya ce ya biyo Rarara kuɗin ne sanadiyyar wayoyi da ya ke karɓa a wajen sa ya na raba wa mutane. Ya ce daga ƙarshe ya ƙi biyan shi kuɗin, kuma ya bi duk wata hanya da zai bi amma kuɗin sun ƙi fita.
A zaman kotun da ya gabata a makon jiya, kotun ta bayyana rashin gamsuwa kan yadda Rarara ko lauyoyin sa su ka gaza amsa sammacin da aka aika masa.
A wata sanarwa da ya bayar, kakakin manyan kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Malam Muzammil Ado Fagge, ya bayyana yadda Rarara ya dinga wasan ɓoyo da masinjan kotu don kada a ba shi sammaci.
Ya ce: “Wannan ƙara ce wadda Muhammad Ma’aji ya shigar da Rarara, kuma ƙara ce wadda akwai mu’amulla da shi har ta naira miliyan goma kuma ya yi ya yi ya ba shi ƙuɗin amma ya ƙi.
“Don haka mun yi amfani da doka da oda ta 9, 2021 da ta yi magana cewa idan aka nemi mutum don a ba shi sammaci ba a gan shi ba to za a iya yin amfani da shafukan sada zumunta don sanar da shi ko kuma a liƙa masa a gidan sa.
“Shi wannan mawaƙin sai wasan ɓuya ya ke yi da jami’in mu don ya ba shi sammacin amma ya ƙi yarda su haɗu, shi ya sa mu ka nemi mai unguwar sa da kuma shaidu mu ka liƙa masa a gidan sa da ke Zoo Road, domin tabbatar da bin doka wajen isar masa da saƙon kotun.”
To amma dai a yau lauyoyin Rarara sun bayyana a ƙarƙashin jagorancin Barrister G.A. Badawi, inda su ka nemi a ba su dama su yi nazarin tuhumar da ake yi wa mawaƙin domin su yi martani.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Halhaltul Khuza’i Zakariya, ya ba su dama, inda ya sanya Litinin mai zuwa, 17 ga Afrilu, 2023 a matsayin ranar da za a koma kotu domin ci gaba da shari’ar.