• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hukumar ‘yan sanda ta sallami jami’an ta da ke kare Rarara

by DAGA ABBA MUHAMMAD
April 13, 2023
in Labarai
0
'Yan sanda ukun da aka kora daga aiki

'Yan sanda ukun da aka kora daga aiki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR ‘yan sanda ta Nijeriya (NPF) ta kori wasu jami’an ta uku daga aiki waɗanda su ke tsaron lafiyar mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a bisa laifin rashin iya aiki.

A ranar Juma’a, 7 ga Afrilu, 2023 ne wani bidiyo ya ɓulla a soshiyal midiya inda aka ga ‘yan sandan su na harba bindiga sama a garin Kahutu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ɗanja a Jihar Katsina lokacin da Rarara ya je raba kayan tallafin azumi.

Sun yi haka ne don su tarwatsa cincirindon matasa da su ka taso wa mawaƙin a lokacin da ya ke shirin komawa Kano.

‘Yan sandan, waɗanda su na aiki ne a Sashen Kare Lafiya na Musamman (Special Protection Unit, SPU, Base 1) da ke Kano, su ne Sufeto Ɗahiru Shu’aibu, Saje Abdullahi Badamasi, da Saje Isah Ɗanladi.

A sanarwar da Kakakin NPF, Mista Muyiwa Adejobi, ya fita a jiya Alhamis, wadda mujallar Fim ta samu kwafe, ya ce: “An kori jami’ai uku da ke SPU Base 1 Kano daga aiki saboda laifuffukan ɗabi’ar rashin hankali da rashin iya sarrafa bindiga, nuna ƙarfin ikon da bai dace ba, babban rashin ɗa’a, da ɓarnar lafiyayyen albarushi.”

Ya ce korar tasu ta biyo bayan kukan da aka kai wa hukumar da kuma binciken da ta yi kan al’amarin.

A cewar Adejobi, duk su ukun an gurfanar da su a gaban kotun ‘yan sanda wadda Babban Alƙalin Rundunar ‘Yan Sanda, wato Force Provost Marshal, ya jagoranta.

Abin da su ka aikata, ba su kula da haɗarin da ka iya samun jama’ar da ta taru a wajen ba, ciki har da ƙananan yara, inji shi.

Kakakin ya ce: “Abin da su ka yi ba ma kawai babban laifi ba ne da kuma rashin iya aiki, a’a, abin tozarci ne ma ga Hukumar ‘Yan Sanda da ma ƙasar nan baki ɗaya.” 

Ya ce saboda haka NPF na gargaɗin jami’an ta da ko yaushe su riƙa gudanar da aikin su bisa dokokin da aka shimfiɗa don gudun hukunci.

Loading

Tags: 'yan sandaDauda RararakoraMuyiwa Adejobitallafitsaron lafiya
Previous Post

Shari’a kan zargin zamba cikin aminci ta N10.3m: Lauyoyin Rarara sun gurfana a kotu

Next Post

Labarin wai na mutu ƙarya ce aka yaɗa, inji Al-Amin Ciroma

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Malam Al-Amin Ciroma

Labarin wai na mutu ƙarya ce aka yaɗa, inji Al-Amin Ciroma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!