ƘUNGIYAR Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta yi kira ga sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), da ya yi tuƙuru ta yadda zai ba maraɗa kunya.
Ƙungiyar ta nuna masa cewa zai yi hakan ne ta hanyar cika alƙawuran da ya yi wa jama’ar jihar a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Waɗannan shawarwari su na ƙunshe ne a cikin takardar taya gwamnan murna wadda MOPPAN ta raba wa manema labarai tare da sa-hannun Sakatare-Janar na ƙungiyar, Malam Salisu Mu’azu.
A fassarar takardar da ta yi, mujallar Fim ta ruwaito Salisu ya na cewa: “Ran ka ya daɗe, a madadin shugabanni da membobin Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), mu na taya ka murnar zama Gwamnan Jihar Kano.
“Nasarar ka nasarar mu ce baki ɗaya, ba tare da kula da jam’iyyar siyasar mutum ba.
“Mu na addu’ar Allah ya sa kada kwaɗayin dukiya da neman wawurar kuɗin jama’a su dakushe zurfin basirar da aka san ka da shi.
“Zamowar ka gwamna babbar alama ce da ke nuna cewa yanzu siyasa ta na komawa wajen ba da mulki ga wanda ya dace.
“Alƙawuran da ka yi na sake haɓaka Kano ya ƙunshi buƙatar dukkan jama’a kuma mu na fatan za ka fara aiki gadan-gadan a yayin da ka tunkari wannan aiki mai wahala.
“Aikin da ke gaba ya na da yawa to amma fatan alherin kowa ya ke yi maka zai sa ka ga aikin da ɗan sauƙi, don haka mu ke fatan za ka yi amfani da wannan damar ka yi wa Kanawa abin da za su yi alfahari da kai.
“Ka cika alƙawarin da ka ɗauka. Ya kamata a ga bambanci mai kyau a dukkan faɗin jihar.
“Hanya mafi dacewa ta gode wa jama’ar Kano kan wannan amincewa da su ka ba ka ita ce ka dage sosai wajen cika wa jama’a alƙawuran da ka yi masu a lokacin yaƙin neman zaɓe.
“Mu na kira a gare ka da ka yi ƙoƙari ka bambanta da mulkin baya. Mutane sun ba ka matuƙar amincewa da yarda, don haka mu na fatan ba za ka ba da kunya ba.
“Mu na ƙara taya ka murna, ran ka ya daɗe, kuma mu na gode maka saboda dagewar ka da zama kaifi ɗaya da kuma gwarzantakar da aka san ka da ita.
“Aiki yanzu ya fara! Lokaci ya yi da za ka yi abin tarihi.”
A wata sabuwa kuma, ƙungiyar ta MOPPAN ta taya sabon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, murna.
A takardar da Salisu Mu’azu ya rattaba wa hannu, ƙungiyar ta ce: “Mai girma Shugaban Ƙasa, ran ka ya daɗe, a bisa zaɓen ka da aka yi na ɗare karaga mafi girma a ƙasar nan, mu shugabanni da ‘ya’yan Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) mu na matukar farin cikin miƙo maka saƙon taya murna tare da yi maka fatan alheri don samun nasara wajen babban aikin da ka sa a gaba.
“Mu na tabbatar maka da cewa a shirye mu ke da mu yi aiki tare da kai wajen haɓaka masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya.
“Mu na yi maka fatan alheri da girmamawa, ya mai girma Shugaban Ƙasa.”