• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 5, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

Nazari

by Barista Badamasi Suleiman Gandu
July 5, 2025
in Nijeriya
0
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dakta) Muhammadu Sanusi II

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RANAR 23 ga Mayu 2024 ta kasance rana mai muhimmanci a zukatan al’ummar Jihar Kano. A wannan ranar ce Allah Maɗaukaki ya kawo ƙarshen rashin adalcin da marasa kishin Kano suka yi, inda Allah ya maida wa mai haƙƙi haƙƙin sa, wato ya maida Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar mulkin Masarautar Kano.

Mayar da Khalifa Muhammadu Sanusi II matsayin sa a Gidan Dabo ya sa ɗaukacin al’ummar Kano masu kishin jihar su da masarautar su murna da farin ciki sosai. Kai, ba su kaɗai ba, har da masu yi wa Kano fatan cigaba daga sassa daban-daban cikin duniya, duk sun cika da farin ciki.

Tun bayan maida shi kan karagar mulkin Kano, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya aiwatar da muhimman tsare-tsaren ƙara wanzar da haɗin kai a tsakanin dukkan ‘yan jinin sarautar Kano, wato Gidan Dabo. Ya sake farfaɗo da Masarautar Kano, martaba da darajar masarautar ya ƙara haskaka duniya. Haka kuma wannan tasiri ya haifar da ƙaruwa da bunƙasar tattalin arzikin wannan ƙasaitacciyar jiha, kamar yadda za a gani a ƙasa:

1. Fannin Bunƙasa Tattalin Arziki:

Sarki Muhammadu Sanusi II ya kasance jajirtacce ainun wajen zaburaswa da haskaka duniya, Najeriya da Kano hanyoyin kawo ci gaba da bunƙasar tattalin arziki.

  • Tasiri A Tattalin Arzikin Ƙasa:
    Sarki tare da Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman da Shugaban Hukumar Bunƙasa Hannayen Jari ta Jihar Kano (Kano-Invest) da wasu da dama, sun wakilci Najeriya a Hanyoyin Bunƙasa Jari da Inganta Cinikayya a Afrika, wato “Financing Investment and Trade in Africa.” An gudanar da wannan taro a Tunis, babban birnin Tunisiya.

Haka kuma wannan ƙasaitacciyar tawaga da ta wakilci Nijeriya a wurin taron, ta gana da Ministan Cinikayya da Bunƙasa Jari na Tunisiya, inda bijiro da hanyoyin da ƙasashen biyu za su haɗa ƙarfi wajen bunƙasa cinikayya wanda ba a ɗirka haraji a faɗin Afrika, wato ‘African Continental Free Trade Area’ (AfCFTA).

2. Shirin Bunƙasa Tattalin Arzikin Kano:

A ƙarƙashin wannan shiri (Kano-Centric Economic Initiatives), Saraki Muhammadu Sanusi ya jagoranci tawaga-tawaga, domin ƙoƙarin samo manyan masu sha’awar haɗin gwiwar zuba jari wuraren da suka haɗa da Hukumar Bunƙasa Ƙasashen Afrika, wato African Union Development Agency (AUDA) da NEPAD, domin haɗin gwiwa da Jihar Kano, ta yadda za su taimaka wajen koya dabarun inganta sana’o’in hannu, zuba jari da tsare-tsaren inganta tattalin arziki.

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya zauna da cibiyar ƙwararru ta bunƙasa tattalin arzikin Afrika da ke Tunisiya, wato Tunisia Consortium for African Development (TUCAD), domin tattauna haɗin gwiwar samar da makamashi tare da kamfanin Enernet Pro a Kano. Wannan wata hoɓɓasa ce ta ganin an samar da wutar lantarki a Kano.
  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya gana da Shugabar Hukumar Zuba Jari ta Tunisiya (Tunisia Investment Authority), Uwargida Namia Ayadi, domin ƙoƙarin samar da hanyoyin shigo da hannayen jari a Jihar Kano.

To irin waɗannan hoɓɓasa da Sarki ke yi na ƙara nunawa da tabbatar da irin tasirin da yake da shi a duniya, a matsayin sa na tauraron wayar da kai don samun nasarar Shirin Wanzuwar Nasarorin Muradun Ƙarni na Sustainable Development Goals, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta naɗa shi.

Sarki Muhammadu Sanusi II

3. Farfaɗo Da Darajar Masarautar Kano Da Gidajen Sarautar Kano:

Daga cikin muhimman ayyukan ci gaba da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya samar tsakanin 2024-2025, shi ne ci gaba da farfaɗo da tsarin Masarautar Kano tare da gidajen sarautar Kano, aikin da ya fara tun mulkin sa na farko a 2014 zuwa 2020. Tsawon shekaru masu yawa dai waɗannan gidajen sarauta sun zama tamkar saniyar-ware.

Wannan kuwa ya ƙunshi sake dawo da sarautun da kowane Gidan Sarauta ya gada, wasu fiye da shekaru ɗari da suka shuɗe. Hakan kuwa ya ƙara ƙarfafa tarihin masarautar, sannan kuma ya jaddada tsarin tafiya tare da kowane Gidan Sarauta. Ga misali a nan:

i. Farfaɗo Da Gidan Sarautar Sarkin Kano Usman:

Wannan gidan sarauta ya kasance ba a dama harkokin mulki a Gidan Dabo da ahalin sa, tun bayan rasuwar Mustapha Ɗanmakwayo cikin 1863. Tsawon shekaru 161 babu wani daga cikin jinin sa da ya riƙe wata sarauta, har sai yanzu da Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Suleiman Lawal sarautar Barayan Kano.

ii. Gidan Sarautar Sarki Tukur:

Rabon wannan gidan Sarauta da riƙe wani muƙamin sarauta, tun bayan rasuwar Sarkin Kano Muhammadu Tukur cikin 1895. Amma yanzu bayan shekaru 129, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Auwalu Mudi sarautar Ɗanmalikin Kano.

iii. Gidan Sarautar Alu Abdullahi Maje Karofi:

Shi ma wannan gidan sarauta ya kasance saniyar-ware tun daga 1975. Wato daga shekarar tsawon shekaru 49 kenan ahalin wannan gida bai riƙe wata sarauta a Kano ba. Amma yanzu Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Bashir Mahe sarautar Dallatun Kano, kuma Hakimin Sharaɗa.

iv. Gidan Sarautar Galaduman Kano Yusuf:

Wannan gidan sarauta ya kasance saniyar-ware tun daga 1965, tsawon shekaru 59 ba su riƙe wata sarauta a Kano ba, sai da Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Abba Yusuf (kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf) sarautar Ɗanmakwayon Kano.

v. Iyalan Ɗanburan Haruna:

Shi Ɗanburan Haruna ya kasance ɗa ne ga Sarki Abdullahi Maje Karofi. Ya rasu cikin 1932. To a tsawon shekaru 92 bayan rasuwar sa, babu wani ahalin sa da ya sake riƙe wata sarauta, har sai da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Mukhtar Ibrahim Bello sarautar Falakin Kano.

vi. Gidan Galadiman Kano Isyaku:

Galadima Isyaku ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ne. Ɗan’uwan sa Sarkin Kano Alu ya naɗa shi Galadima. Ya rasu cikin 1900, kuma tun daga lokacin babu wani jinin gidan Galadima Isyaku da ya sake riƙe wata sarauta tsawon shekaru 124. Har sai lokacin da Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Abdulƙadir Mohammed Balarabe sarautar Zannan Kano.

vii. Gidan Wazirin Kano Ahmed Mai Shahada:

Wazirin Kano Ahmed Mai Shahada ɗa ne ga Abdullahi Maje Karofi. An kashe shi a gumurzun yaƙi da Turawan mulkin mallaka cikin 1903. Kuma daga shekarar ba wani ɗan gidan sa da aka naɗa wata sarauta, tsawon shekaru 121. Har sai lokacin da Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi sarautar Galadiman Daji.

viii. Gidan Sarautar Sarkin Kano Muhammadu Inuwa:

Bayan rasuwar Sarkin Kano Muhammadu Inuwa cikin 1963, Sarkin Kano Ado Bayero ya gaje shi. Amma daga nan babu wani ɗan gidan sarautar Sarki Inuwa da ya sake yin sarauta, sai hawa mulki na farko na Sarki Muhammadu Sanusi II, inda ya naɗa Alhaji Yahaya Inuwa Abba sarautar Ɗanmajen Kano, kuma Hakimin Gwale. Yanzu kuma cikin wannan shekarar farko da Sarki Muhammadu Sanusi II ya koma kan mulki, ya ɗaga likkafar Ɗanmaje ta yi gaba, ya naɗa shi Ɗan Galadima, kuma Hakimin Dala.

ix. Gidan Ɗanlawan Ayuba:

Ɗanlawan Ayuba ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ne. Shi ne mahaifin Turakin Kano Abubakar. Turakin Kano Abubakar ya yi Turaki zamanin Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1903-1919). Daga wancan zamanin babu wanda ya sake riƙe wata sarauta a gidan, har sai da Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Aminu Sadik sarautar Zanna. Daga nan kuma likkafar sa ta yi gaba zuwa Bunun Kano, Hakimin Rijiyar Lemo a cikin wannan shekara ɗaya bayan komawar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.

Waɗannan misalai sun nuna irin nasarori da ƙoƙarin da Mai Martaba Sarki ya yi wajen gyara rashin adalcin da ya wanzu kan wasu gidajen sarauta a baya. Hakan kuma wani gagarumin cigaba ne wajen ƙara ƙarfafa ginshiƙin tsarin Masarautar Kano.

4. Dawo Da Al’adar Rangadi A Masarautar Kano:

Rangadi ziyara ce sarki kan yi a yankunan masarautar sa. Daɗaɗɗiyar al’ada ce, wadda aka daina tun cikin 1980. Sai dai an dawo da yin rangadi cikin 2004, bayan ƙaddamar da shirin A Daidaita Sahu, wanda gwamnan lokacin Ibrahim Shekarau ya ƙirƙiro. A wancan lokacin, marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya karɓi shirin hannu bibbiyu, inda ya yi rangadin dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano domin ƙarfafa shirin a zukatan jama’a.

Domin ƙarfafa nagartacciyar gwamnati da kuma ganin an farfaɗo da kyawawan al’adu, sai Sarki Muhammadu Sanusi ya ƙirƙiro hakimai 12, waɗanda kowanen su aka naɗa a sabbin masarautu ko yankuna, waɗanda suka haɗa da:

i. Malam Bashir Mahe, Dallatun Kano, Hakimin Sharaɗa.

ii. Alhaji Shehu Kabiru Bayero, Barde Ƙerarriya, Hakimin Ɗorayi.

iii. Alhaji Aliyu Harazumi, Ɗan’amar, Hakimin Gobirawa.

iv. Alhaji Aminu Sadiq, Bunun Kano, Hakimin Rijiyar Lemo.

v. Alhaji Mujitaba Abubakar, Sarkin Yaƙin Kano, Hakimin Darmanawa.

vi. Alhaji Sanusi Abubakar, Ɗan Akansan Kano, Hakimin Zaura Babba.

vi. Jakada Ahmed Umar, Jarman Kano, Hakimin Mariri.

viii. Alhaji Ali Ado Bayero, San Turakin Kano, Hakimin Kunya.

ix. Alhaji Abdulƙadir Balarabe, Zannan Kano, Hakimin Jogana.

x. Alhaji Idris Sanusi Bayero, Sarkin Sulluɓawa, Hakimin Rimi.

xi. Alhaji Mansur Isa, Sarkin Kudu, Hakimin Gabasawa.

xii. Ibrahim Ado Bayero, Ɗan Ruwatan Kano, Hakimin Kawaji.

Waɗannan sababbin Hakimai ba kawai na jeka-na-yi-ka ba ne; suna zaman cikakkun wakilan Sarki a unguwanni ko garuruwan da aka naɗa su. Suna aiki ne tare da Dagatai da Masu Unguwanni a yankunan su. Muhimman ayyukan su sun haɗa da gano irin yanayin rayuwar da al’umma ke ciki, tare da kai wa Sarki rahoton bayanan da suka binciko. Wannan tsari kuwa yana tabbatar da wanzuwar nagartacciyar hulɗa tsakanin mai mulki da al’ummar sa.

Saboda haka wannan tsari za a iya cewa tamkar wani sabon salon Rangadi ne a zamanance, wato tsari wanda masana tarihin Musulunci suka gano cewa ya samo tushe tun daga zamanin Khalifa Umar ibn al-Khattab (Radiyallahu Anhu). Fa’idar sake farfaɗo da wannan tsari ya haɗa da:

  • Ƙarfafa Tsarin Shugabanci A Yankunan Karkara Ko Cikin Jama’a: A nan, jajirtattun hakimai su na kai wa Masarauta haƙiƙanin bayanan ƙalubale da buƙatun al’umma, wanda hakan na ƙara karsashin yadda ake gudanar da mulki.
  • Ƙara Kusanci Da Jama’a: Samun hakimai a yankunan su na ƙara haifar da fahimta da samun damar ganawa a tsakanin masu mulki da jama’a, wanda hakan na ƙara sa al’umma su yin amanna da kuma jin cewa tabbas ana jan su a jika.
  • Damar Gaggauta Aiwatar Da Shirye-shirye Ko Daidaita Al’amurra: Irin wannan tsari wanda Hakimai ke kai wa Sarki rahoton bayanan yankunan su kai-tsaye, ya na samar da damar gaggauta gano inda wata matsala take, sannan ana shawo kanta tare da daƙile wasu ƙananan matsaloli domin hana su ruruwa har su ta’azzara.
  • Adana Kyawawan Al’adu: Rangadi zai hanya ce ta ƙarfafa kyawawan al’adu da tarihin Masarauta, bayyana asali da tushen al’umma tare da zama wata mahaɗar tsarin mulki na gwamnati da nagartattun al’adu da kyawawan ɗabi’u.
  • Wanzar Da Haɗin Kai Da Kwanciyar Hankali: Irin yadda al’umma ke ganin yadda ake tafiyar da tsarin jagorancin su musamman kai-tsaye ta hanyar yin rangadi, hakan zai ƙara samar da kwanciyar hankali, zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Kano.
  • Rangadi Zai Ƙara Bijiro Da Hanyoyin Cigaban Jama’a: Kasancewa Hakimai su ne hanyoyin da ake gano wurare da ɓangarorin da ke buƙatar a hanzarta sama musu ayyukan cigaba, sun kuma kasance masu sa-ido kan ayyukan inganta rayuwar jama’a da aka aiwatar.

Idan har za a iya yin amfani da wannan tsari a faɗin ƙasar nan, tabbas za a samar da hanyar warware matsalolin da suka dabaibaye jama’a tun daga tushe.

Saboda haka ina yin kira ga gwamnati ta sake duba wasu tsaren-tsaren gudanar da mulki tun na kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, ta rungumi wannan tsari, domin inganta hanyoyin gudanar da nagartaccen jagoranci.

5. Kyakkyawan Jagoranci Da Sasanci:

Sarki Muhammadu Sanusi II har yau bai nuna gajiyawa ba wajen samar da kyakkyawan misalin jagorancin al’umma, wanda ya kasance abin koyi. Misali wajen ƙarfin halin sa kan nuna yafiya da kuma sasanta saɓani.

Babban misali a nan shi ne naɗa Jamilu Sani Umar sarautar Dagacin Ƙauyen Ganduje. Jamilu ɗan’uwa ne ga tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Amma duk da turnuƙewar hayaƙin siyasar da aka yi fama a Kano a baya, Sarki bai dubi wannan ba. Wannan kuwa irin tawakkalin sa da kyakkyawar zuciyar yafiya, domin samar da haɗin kan al’ummar sa.

Wannan karimci da Sarki ya yi ne ya kai ga iyalan Ganduje yin mubaya’ar amincewa da Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin halastaccen Sarkin Kano, maimakon su tuɓaɓɓen Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

6. Farfaɗo Da Wasu Kyawawan Al’adun Masarautar Kano:

i. Domin ganin masarauta ta ƙara samun karsashi da martaba, Sarki ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa masamman wajen jawo jama’a a jika, ta hanyar karɓar taron ɗaurin auren ɗan Sanata Rabi’u Kwankwaso da ‘yar Alhaji Barau Mangal a Fadar sa.

ii. Sarki Muhammadu Sanusi II ya jajirce wajen hidimar ɗaɓbaƙa addinin Musulunci, ta hanyar halartar saukar Alƙur’ani da ƙarfafa taron masabaƙar Alƙur’ani Mai Girma.

iii. Yana tabbatar da cancanta wajen tantance limaman masallatai. Ya na ƙoƙari ƙwarai wajen sasanta saɓani ko rashin fahimta.

iv. Ya Ɗabbaƙa Hawan Babban Ɗaki: Wata kyakkyawar al’adar da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya ɗabbaƙa ita ce Hawan Babban Ɗaki. Hawa ne da Sarki ke yi domin zuwa gaishe da mahaifiyar sa, saboda neman albarka da tubarrakin mahaifiya. Hakan nuni ne ga matasa cewa su riƙe iyaye hannu bibbiyu tare da yi masu biyayya.

v. Mai Martaba Sarki ya kasance yana limancin Sallar Idi, Sallar Juma’a da Sallar Janaza. Hakan kuwa wasu hanyoyi ne na ƙara zaburar da matasa tashi su nemi ilmi, kuma su riƙa shiga ana gudanar da ayyukan ibada tare da su a cikin jama’a.

vi. Haka nan Sarki yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro, ta hanyar ganawa da masu riƙe da muƙaman sarauta, ƙungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta tsaro a faɗin Jihar Kano.

Allah ya ja zamanin Sarki. Allah ya kawo dauwamammen zaman lafiya a Kano.

* Barrister Badamasi Suleiman Gandu ya rubuto daga Kano.

Imel: abulhanan13@gmail.com

08038936183

(Editan Rubutu: Ashafa Murnai Barkiya)

Loading

Tags: Masarautar KanoSarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Previous Post

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!